Kwankwaso: Abin da ya sa Peter Obi ba zai iya lashe zaben shugaban kasa a Jam’iyyar LP ba
- Rabiu Musa Kwankwaso ya ce a yadda ake tafiya, da kamar wahala Labour Party ta kafa gwamnati
- Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ce magoya bayan Labour Party duk sun dankare ne a yanki guda
- Dokar kasa ta tsara cewa kuri’un bangare daya ba zai iya sa a nada wani ya zama shugaban Najeriya ba
Abuja - Rabiu Musa Kwankwaso mai neman zama shugaban Najeriya a karkashin jam’iyyar adawa ta NNPP, ya ce Labour Party ba za ta iya lashe zabe ba.
A wata hira da aka yi da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a shirin siyasar nan na Politics Today a gidan talabijin na Channels, ya yi magana a kan shirin zaben 2023.
Legit.ng Hausa ta bibiyi wannan hira, inda aka ji Kwankwaso yana magana a game da Peter Obi, duk da bai fito ya ambaci sunan ‘dan takaran LP karara a hirar ba.
An ji fitaccen ‘dan siyasar yana cewa a 2023, jam’iyyar LP ba za ta iya kafa gwamnati a Najeriya ba.
Kamar yadda ‘dan takaran na jam’iyyar NNPP yake cewa, jam’iyyun PDP da APC ba za su samu kuri’a daga Kudu maso gabas ba, saboda tasirin Peter Obi da LP.
Hakan ta sa Kwankwaso yake ganin akwai bukatar Obi ya hada-kai da NNPP wanda ta yi yado a yankin Arewacin Najeriya, domin su karbe shugabancin Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ba haka doka ta ce ba - Kwankwaso
“Mu na sane a kafafen sadarwa na zamani, matasa da matan da suka fito daga Kudu maso gabas, su na kokarin ganin sun karbi shugabancin kasa.”
“Amma maganar gaskiya, ko duka ‘yan yanki guda za su zabi mutum daya, a doka ba zai iya zama shugaban kasa ba, da gan-gan aka tsara hakan.”
- Rabiu Musa Kwankwaso
Daily Trust ta rahoto Kwankwaso yana cewa tsarin mulkin ya kawo wannan ne domin a tafi da kowa.
Zai yi kyau a tafi da Ibo a 2023
Baya ga haka, an ji Kwankwaso yana cewa tun yanzu mutanen Kudu maso gabas su na kukan ba a damawa da su, ina ga APC ko PDP ta karbi mulki a badi.
A Arewa, 'dan takaran yana ganin cewa NNPP da ake yi wa taken mai kayan dadi, za ta samu karbuwa, duk da ya yarda ba a gane kan mutanen yankin.
“A yadda ake tafiya, jam’iyyar LP ba za ta iya cin zabe ba domin magoya bayanta ‘yan yanki guda ne, kuma kuri’un nan ba za su ba mutum mulki ba."
- Rabiu Musa Kwankwaso
Taron dangin NNPP da LP
A baya an ji rahoto da ya nuna kokarin da ake yi na samun hadin-kai tsakanin Labour Party da New Nigeria Peoples Party na nan har zuwa makon da ya wuce.
Jagororin jam’iyyu hamayyar sun tabbatar da cewa ana cigaba da magana domin a bullowa 2023. Dr. Agbo Major da Dr. Yunusa Tanko duk sun tabbatar da haka.
Asali: Legit.ng