2023: Gwamnonin APC sun zauna, sun yi shawarwari kan yankin da zai kawo abokin tafiyar Tinubu
- Jam'iyyar APC na ci gaba da shawarar wanda za a zabi ya zama abokin gami ga Bola Ahmad Tinubu a zaben 2023
- Yayin da ake kara fuskantar buga gangar siyasa ta zaben 2023, Tinubu bai zabi takamaiman mataimaki ba
- Shiyyar Arewa maso Yammacin Najeriya ta magantu, ta ce ita tafi cancanta ta kawo abokin tafiyar Tinubu
Gwamnonin jam’iyyar APC daga yankin Arewa maso Yamma da sauran shugabannin shiyyoyin sun gana kan kujerar mataimakin shugaban kasa na jam’iyya mai mulki.
Masu ruwa da tsaki na yankin Arewa maso Yamma sun yi takama da cewa shiyyar ita ce yankin siyasa mafi girma a kasar, inda suka kara da cewa za samar da karin kuri’u ga jam’iyya mai mulki a zabukan 2015 da 2019.
Ana ci gaba da neman wanda zai y takarar mataimakin shugaban kasa tare da Bola Ahmed Tinubu, watanni biyu kacal kafin buga gangar siyasa, rahoton Daily Trust.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Sanarwar bayan taron nasu ranar Alhamis a Abuja, mai dauke da sa hannun mataimakin shugaban jam’iyyar APC na shiyyar (Arewa-maso-maso-Yamma), Salihu Mohammed Lukman, ya ce gwamnonin APC da ‘yan takarar gwamna da ministoci daga jihohin shiyyar ne suka halarci taron.
Wani bangare na sanarwar ya ce:
“Taron ya yi maraba da shirin fara wannan taron tuntuba da yake da matukar muhimmanci wajen karfafa jam’iyyar APC a shiyyar Arewa maso Yamma da kuma inganta harkokin shugabanci da hadin kai a shiyyar.
“Taron na shiyya ya yi maraba da nasarar kammala zaben fidda gwani a matakin jiha da na kasa baki daya.
"Mahalarta taron sun amince da kalubalen da ke fuskantar wasu sassan jam'iyyar na jihohi tare da kudura aniyar inganta kokarin yin sulhu a matsayin wani muhimmin abu cikin gaggawa.
“Taron ya nuna irin gudunmawar da yankin Arewa-maso-Yamma ya bayar wajen dasa jam’iyyar APC da ci gabanta da kuma samun damar gudanar da zabe, inda yankin Arewa maso Yamma ya bayar da kusan 39% na kuri’un da APC ta samu a zaben shugaban kasa na 2019 da 2015.
"Saboda haka, shiyyar ta yanke shawarar tattara bukatunta da abubuwan da ke damun ta tare da hulda da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar."
Ana suya ana manta albasa
Sai dai, wani mamban APC a karamar hukumar Deba, Yunusa Umar Shinga ya koka kan yadda yankin Arewa maso Gabas ta zama abar mancewa a idon manyan APC.
Ya shaidawa wakilin Legit.ng Hausa da ke jihar Gombe cewa, matasan APC sun sha kira cewa a duba a zabi gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum domin wannan aikin.
Ingiza mai kantu: Kungiyar Yarbawa ta zargi Arewa da kullawa Tinubu tuggu a zaben shugaban kasa na 2023
Ya ce:
"A Najeriya babu wanda bai san Zulum ba. Idan ana neman sananne da zai kawo kuri'u ne to lallai ya cancanta.
"Siyasa abu ne na jama'a ba wai kawai abin da ya faru ko rige-rige bane. Ya kamata 'yan Arewa maso Yamma su gane, ana suya ana manta albasa ne.
"Ba a cika zabi mutane daga yankin mu ba, don haka ni na yi mamaki da Tinubu ya zabi Alhaji Kabir Masari tun farko."
A wani labarin, jam’iyyar APC mai mulki ba shirya wasa ba, domin ta shirya kaddamar da shafin yanar gizo domin hada kan matasa kafin zaben shugaban kasa na 2023.
Kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito, shugaban matasan jam’iyyar APC na kasa, Dayo Israel ya bayyana shirin ne a ranar Laraba, 29 ga watan Yuni a Abuja.
Mista Israel ya bayyana cewa sabon shirin an yi shi ne domin tabbatar da damawa da matasa a harkokin siyasar jam'iyyar. Ya ce dandali ne da ake son amfani dashi wajen jawo hankalin matasa zuwa jam’iyyar.
Asali: Legit.ng