PDP ta dakatar da shugabanta a wata jihar arewa, ta bayyana dalili mai karfi
- Jam’iyyar PDP reshen jihar Borno ta dauki mummunan mataki a kan shugabanta, Alhaji Zannah Gadama
- An dai dakatar da Gadama a yau Alhamis, 30 ga watan Yuni kan zargin yiwa jam’iyyar zagon kasa da kuma almubazaranci da kudade
- Jam’iyyar ta kuma maye gurbinsa da mataimakinsa, Bunu Garba Satomi wanda zai karbi ragamar jagoranci nan take
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Borno - Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) reshen jihar Borno a ranar Alhamis, 30 ga watan Yuni, ta dakatar da shugabanta, Alhaji Zannah Gadama, kan cin dunduniyar jam’iyyar.
Hakan na kunshe ne a cikin wata takarda da aka fitar a karshen wani taron gaggawa da aka kira dauke da sa hannun bai ba PDP reshen jihar shawara kan doka, Mista Abdu Jidda a Maiduguri a ranar Alhamis, jaridar The Nation ta rahoto.
Sanarwar ta ce:
“Don haka an dakatar da shugaban jam’iyyar na tsawon wata daya, yayin da mataimakinsa, Malam Bunu Garba Satomi zai karbi jagoranci daga hannunsa nan take.”
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ya ce an samu shugaban jam’iyyar da hannu wajen yiwa jam’iyyar makarkashiya.
Jidda ya ce:
“Baya ga karya sashe na 58 (a, b, c, d, f, da j) na kundin tsarin mulkin jam’iyyar na 2017 da aka gyara, ta hanyar kin kiran taro, almubazzaranci da yiwa kudade jam’iyyar rikon sakainar kashi, Gadama da wasu daga cikin na kusa da shi sun tsunduma cikin aikata ayyukan da suka sabawa jam’iyya, wanda hakan ya hana jam’iyyar damar samun duk wani mukami na zabe a ‘yan baya-bayan nan a jihar.
“Don haka, bayan dogon nazari a yau, mun samar da mafita uku, bisa ga ikon da sashi na 53(3) ya ba wa wannan taro, an dakatar da Zanna Gadama ba tare da bata lokaci ba har na tsawon wata daya zuwa lokacin da za a ci gaba da bincike.
“Abu na biyu, mataimakin shugaban jam’iyyar a jihar wato Bunu Garba Satomi ya karbi shugabanci a matsayin rikon kwarya a tsawon lokacin dakatarwar.
“Abu na uku, muna kira ga shugabancin jam’iyyarmu, PDP da su dauki matakin gaggawa sannan su dawo da jam’iyyar reshen jihar Borno hayyacinta."
Ya kara da cewa:
“Mutanen Borno a yau suna tsananin bukatar shugabanci mai kyau kuma suna duba zuwa ga PDP a matsayin jam’iyyar da za ta iya ceto su daga kangin talauci, rashin aiki da rashin adalci.”
Taron ya samu halartan mambobin kwamitin NWC, shugabannin da sakatarorin dukkanin kananan hukumomi 27 na jihar da sauransu, rahoton Daily Post.
Zaben Osun: Ba a ga Tambuwal, Wike, Fintiri da sauran gwamnoni ba yayin da PDP ta kaddamar da kamfen dinta
A wani labarin, mun ji cewa a ranar Laraba, 29 ga watan Yuni ne jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), ta kaddamar da kwamitin kamfen dinta na zaben gwamnan jihar Osun.
Za a gudanar da zaben gwamnan na Osun ne a ranar 16 ga watan Yulin 2022, kuma tsohon dan majalisar dattawa, Sanata Ademola Adeleke ne dan takarar jam’iyyar a zaben.
Jam’iyyar PDP ta bayyana gwamnan jihar Bayelda, Douye Diri, a matsayin shugaban kwamitin yakin neman zaben, jaridar The Cable ta rahoto.
Asali: Legit.ng