2023: Tashin hankali a PDP yayin da mambobi 10,000 suka tsallake zuwa APC

2023: Tashin hankali a PDP yayin da mambobi 10,000 suka tsallake zuwa APC

  • Makonni kadan da gudanar da zaben gwamna a jihar Osun, jam’iyyar adawa ta PDP reshen jihar ta gamu da cikas na sauya sheka
  • Akalla mambobi 10,000 ne daga unguwanni daban-daban da kananan hukumomi da mazabun tarayya na jihar suka fice daga PDP zuwa APC
  • Fitattun sunayen wadanda suka sauya sheka sun hada da Wale Ojo, shugaban bangaren PDP na jihar, da Hon Albert Adeogun, abokin takarar dan takarar gwamnan PDP a zaben 2018

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Osogbo, jihar Osun - Akalla mambobin jam’iyyar PDP 10,000 ne aka bayyana cewa sun sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Osun a ranar Litinin, 27 ga watan Yuni.

Jaridar Nigerian Tribune ta ruwaito cewa, an yi wannan biki na sauya sheka ne a filin shakatawa na Nelson Mandela da ke Osogbo, babban birnin jihar.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: An kama wanda ya harbe tsohon hadimin Jonathan, Ahmad Gulak

Legit.ng ta tattaro cewa Hon Wale Ojo, shugaban tsagin PDP na jihar, da Hon Albert Adeogun, dan takarar mataimakin gwamnan PDP a zaben 2018 a Osun, na daga cikin wadanda suka fice daga PDP zuwa APC.

PDP ta yi rashi, APC ta samu kari
2023: Tashin hankali a PDP yayin da mambobi 10,000 suka tsallake zuwa APC | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Wasu fitattun sunayen da suka koma jam’iyyar APC mai mulki su ne tsohon dan majalisar wakilai; Ayodele Asalu (Asler), dan takarar majalisar wakilai a mazabar tarayya ta Ede da kuma Soji Ibikunle, kusan jam'iyyar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An kuma bayyana cewa adadin wadanda suka sauya sheka ya karu a unguwanni daban-daban, kananan hukumomi da kuma mazabun tarayya na jihar.

Ficewar ta zo ne makonni kadan bayan gudanar da zaben gwamna a jihar Osun.

Osun 2022: Dalilin da ya sa muka sauya sheka daga PDP zuwa APC – Wale Ojo

Da yake magana a madadin wadanda suka sauya shekar, Honarabul Wale Ojo ya danganta matakin sauya shekar zuwa jam’iyya mai mulki da bukatar samun daidaito da wata alama ta nagarta da ci gaban Gwamna Oyetola.

Kara karanta wannan

Kayan marmari: Jam'iyyar su Kwankwaso NNPP ta samu mutane miliyan 2 a jihar Borno

Yace:

“Shiga jam’iyyar adawa a Osun tamkar hada karfi da karfe ne da mabarnata. Jam'iyyun da suka gaji asara a jere ba su da darajar da ta cancanta a bi ta ga duk mutumin gaske kuma mai hango jagoranci mai kyau.
"Don haka ne muka zo mu daidaita da alamar daukaka da ci gaba na gwamna Oyetola."

Tsohon dan takarar mataimakin gwamnan PDP Adeogun ya yaba wa Oyetola

A nasa jawabin, Albert Adeogun, dan takarar mataimakin gwamna a jam’iyyar PDP a zaben 2018, ya yaba wa Oyetola bisa yadda ya kawo kwanciyar hankali a rigingimun siyasar jihar, inda ya kara da cewa zaben Oyetola daidai yake da ‘yantar da jama’a.

A kalamansa:

“A yau mun zo ne domin mu hada kai da jam’iyya mai ci gaba don ba da gudummuwa ga gagarumin aikin da ake yi. Muna jinjina wa gwamnan, wanda duk da karancin kudi a jihar ya ci gaba da tafiyar lamurra daidai.

Kara karanta wannan

Masu neman takarar gwamna 3 sun sauya sheka daga APC zuwa PDP a jihar Sokoto

“Lokacin da muke ‘yan adawa, muna da sakonnin gangami masu karfi a kan APC, amma Oyetola ya ji da duk wadannan batutuwa kuma ya kashe dafin PDP. Ya kamata a sanar da kowani dan kasa kuma a fahimtar da shi cewa zaben Oyetola kuri’ar ‘yanci ce."

Omisore ya karbi wadanda suka sauya sheka

Da yake karbarsu zuwa cikin jam’iyyar, Sakataren jam’iyyar APC na kasa, Sanata Iyiola Omisore, ya yi maraba da wadanda suka sauya sheka bisa daukar matakin da ya dace na shiga cikin jirgin ci gaban gwamnatin jihar.

Omisore ya bayyana zabin nasu a matsayin abu mai daraja da kuma tunani mai kyau, sun dawo cikin iyali da ke samar da yanayi na daidaito da adalci.

Da yake jawabi ga wadanda suka sauya sheka da kuma amintattun jam’iyyar, Gwamna Adegboyega Oyetola, ya yabawa sabbin ‘yan mambobin bisa daukar kwakkwaran mataki na inganta siyasarsu, yana mai cewa APC ta yi fice wajen yin adalci.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Jerin Sanatocin APC da Suka Sauya Sheka Zuwa PDP da Wasu Jam'iyyu

2023: Kungiyar matasan APC sun dage, sun ce Zulum ne ya kamata ya yi takara da Tinubu

A wani labarin, kungiyoyin matasa da dama na APC a jihar Bauchi, sun yi kira ga shugabannin jam’iyyar da mai rike da tutar shugaban kasa a zaben 2023, Bola Tinubu da su zabo Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno a matsayin abokin takararsa, rahoton Punch.

Shugaban kungiyar matasan na APC, Malam Shamsuddeen Waziri wanda ya yi wannan kiran ya ce Tinubu da Zulum za su kara wa jam’iyyar riba a zabuka da kuma kara mata damar lashe zaben shugaban kasa mai zuwa.

Kungiyar ta bayyana haka ne a wani taron manema labarai da ta gudanar a Bauchi, inda ta ce bayan nazarin matsalolin tsaro da tattalin arziki da sauran matsalolin da suka dabaibaye Najeriya, sun ba da shawarin a zabi Zulum domin tafiya da Tinubu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel