Zaben Osun: Ba a ga Tambuwal, Wike, Fintiri da sauran gwamnoni ba yayin da PDP ta kaddamar da kamfen dinta

Zaben Osun: Ba a ga Tambuwal, Wike, Fintiri da sauran gwamnoni ba yayin da PDP ta kaddamar da kamfen dinta

  • Jam’iyyar PDP ta kaddamar kwamitin mutum 128 don zaben gwamnan jihar Osun wanda za a yi a ranar 16 ga watan Yuli
  • Gwamna Duoye Diri na jihar Bayelsa ne zai yi jagoranci yayin da Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ke cikin mambobin kwamitin
  • Sai dai kuma, ko sama ko kasa ba a gano yawancin gwamnonin jam’iyyar adawar ba a wajen kaddamar da kwamitin neman zaben

Osun - A ranar Laraba, 29 ga watan Yuni ne jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), ta kaddamar da kwamitin kamfen dinta na zaben gwamnan jihar Osun.

Za a gudanar da zaben gwamnan na Osun ne a ranar 16 ga watan Yulin 2022, kuma tsohon dan majalisar dattawa, Sanata Ademola Adeleke ne dan takarar jam’iyyar a zaben.

Jam’iyyar PDP ta bayyana gwamnan jihar Bayelda, Douye Diri, a matsayin shugaban kwamitin yakin neman zaben, jaridar The Cable ta rahoto.

Kara karanta wannan

An samu mummunan yamutsi a PDP, rikici ya ki karewa a kan abokin takarar Atiku Abubakar

Gwamnonin PDP
Zaben Osun: Ba a ga Tambuwal, Wike, Fintiri da sauran gwamnoni ba yayin da PDP ta kaddamar da kamfen dinta Hoto: PDP Governors In Action
Asali: Facebook

An nada gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo. Aminu Tambuwal na Sokoto, Okozie Ikpeazu na Abia, Nyesom Wike na Ribas, Udom Emmanuel na Akwa Ibom, Ifeanyi Ungwuanyi na Enubu a matsayin mataimakan shugaban kungiyar kamfen din.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sauran mataimakan sune Bala Mohammed na Bauchi, Ahmadu Fintiri na Adamawa, Gowin Obaseki na Edo, da Samuel Ortom na Benue. Sai dai kuma dukkansu basu halarci taron ba.

Wadanda suka halarci taron sun hada da Ifeanyi Okowa, dan takarar mataimakin shugaban kasa na PDP, Darius Ishaku, gwamnan jihar Taraba da sauran mambobin kwamitin uwar jam’iyya.

Da yake magana kafin kaddamar da kwamitin, Umar Damagum, mukaddashin shugaban PDP, ya nuna karfin gwiwar cewa jam’iyyar za ta yi nasara a zaben gwamnan, rahoton Daily Trust.

Ya ce:

“Muna da shahararren dan takara a Osun kuma babu wani dalili da zai hana mu lashe zaben.

Kara karanta wannan

2023: Tashin hankali a PDP yayin da mambobi 10,000 suka tsallake zuwa APC

“Don haka, na yi imani cewa da irin mutanen da ke wannan kwamitin, ina da tabbacin Osun zai zama namu, za ka yi sadaukarwa da dama na aikin da ke gabanka, ka tattauna da masu ruwa da tsaki da suka fusata.”

Buhari ya saki muhimmin sako game da zaben 2023, ya bayyana abun da zai yi

A wani labarin, Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cewar zai kasance a tsaka-tsaki a babban zaben 2023 mai zuwa ba.

Jaridar The Nation ta rahoto cewa Buhari ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, 29 ga watan Yuni, yayin da yake jawabi ga yan Najeriya mazauna Portugal a Lisbon, babbar birnin kasar.

Ya kuma bayyana cewa zai ba hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) cikakken yancin gudanar da zabe na gaskiya da amana.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng