Yanzun Nan: Atiku Abubakar ya magantu kan sabon rikicin da ya ɓarke a jam'iyyar PDP

Yanzun Nan: Atiku Abubakar ya magantu kan sabon rikicin da ya ɓarke a jam'iyyar PDP

  • Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya ce suna cigaba da ɗaukar matakan rarrashin mambobin da suka fusata
  • Tsohon mataimakin shugaban ya ce jam'iyyar zata cigaba da zama tsintsiye maɗaurinki ɗaya don maida hankali kan abinda ke gaba
  • Al'amura sun dagulewa PDP ne tun bayan da Atiku ya zaɓi gwamnan Delta a matsayin mataimaki

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya karya shiru, ya yi magana kan sabon rikicin da ke neman maida hannun agogo baya a jam'iyyar PDP.

A wani sako da ya saki a shafinsa na Facebook, Atiku yace PDP ba zata tarwatse ba, zasu ɗauki matakin shawo kan duk waɗan da ke ganin an yi ba dai-dai ba.

Babbar jam'iyyar hamayya ta shiga sabon zagayen rikici ne bayan ɗan takararta na shugaban kasa, Atiku, ya zaɓi gwamna Ifeanyi Okowa a matsayin abokin takararsa a zaɓen 2023.

Kara karanta wannan

Sabon rikici ya ɓarke a PDP, Babban Jigo ya yi watsi da Atiku, yace wajibi mulki ya koma kudu a 2023

Alhaji Atiku Abubakar.
Yanzun Nan: Atiku Abubakar ya magantu kan sabon rikicin da ya ɓarke a jam'iyyar PDP Hoto: Atiku Abubakar/facebook
Asali: Facebook

Wannan cigaban ya tada kura tare da haifar da saɓani tsakanin manyan jiga-jigan jam'iyyar, yayin da wasu suka fara kiraye-kirayen a tunbuke shugaban PDP na ƙasa, Dakta Iyorchia Ayu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Alamu sun nuna ba abinda ke tafiya dai-dai a jam'iyyar domin sakamakon haka gwamnoni biyu rak cikin 13 ne suka halarci wurin da kwamitin ayyuka NWC ya kaddamar da tawagar yaƙin neman zaɓen gwamnan jihar Osun ranar Laraba.

Wane mataki zasu ɗauka don shawo kan lamarin?

Amma da yake tsokacin kan abubuwan da ke faruwa, Atiku Abubakar, ya ce tuni shiri ya yi nisa na shawo kan mambobin da suka fusata da kuma warware matsalolin da suka taso.

"PDP zata cigaba da zama kai a haɗe, maida hankali kan ayyukan mu, mun fara ɗaukar matakan rarrashin mambobin da suka fusata. Haɗin kai tsakanin jama'ar mu shi na sa a gaba."

Kara karanta wannan

Wata Sabuwa: Mataimakin gwamna ya maka majalisar dokokin jiha a Kotu kan yunkurin tsige shi

"Kudirin haɗa kan Najeriya ya fara ne daga jam'iyyar mu ya matsa zuwa wasu jama'a, daga nan kuma zuwa Al'umma. Kowane gwamna, ɗan majalisa, da sauran zababbu, mambobi da magoya baya, ina girmama su kuma ina ƙaunar su."
"Idan suka yi magana zan saurara, ba sauraro kaɗai nake yi ba, mun ɗauki matakin da ya dace, muna kan ɗaukar matakai kuma haka zamu cigaba da yin abinda ya kamata."

- Atiku

A wani labarin kuma Gwamnan APC ya faɗi babban laifin INEC da ya jawo batan takardun Tinubu

Gwamnan jihar Imo ya zargi hukumar zaɓe da haddasa duk abinda ya biyo baya game da takardun shaidar karatun Bola Tinubu.

Gwamna Hope Uzodinma ya ce tun shekarar 1999 Tinubu ke shiga zaɓe a Najeriya kuma takardun nan b a canzawa suke ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262