Da Dumi-Ɗumi: Fayose ya yi watsi da Atiku, ya ce wajibi mulki ya koma kudancin Najeriya a 2023

Da Dumi-Ɗumi: Fayose ya yi watsi da Atiku, ya ce wajibi mulki ya koma kudancin Najeriya a 2023

  • Sabon rikici ya kunno kai a babbar jam'iyyar hamayya PDP, tsohon gwamnan Ekiti ya yi hannun riga da tsayar da ɗan arewa a 2023
  • Ayodele Fayose, ya ce tsarin mulkin PDP ya tanadi tsarin karɓa-karba, wajibi bayan Buhari a yi adalci, ɗan kudu ya karɓi shugaban ƙasa
  • Fayose na ɗaya daga cikin yan takarar da suka fafata a zaɓen fidda gwanin PDP wanda Atiku Abubakar ya samu nasara

Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya buƙaci mulki ya koma kudancin Najeriya, a cewarsa babu adalci wani ɗan arewa ya karɓi mulki bayan shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya kammala wa'adi biyu.

Fayose, na hannun daman gwamnan Ribas Nyesom Wike, yana ɗaya daga cikin yan takarar da suka fafata a zaɓen fidda gwanin PDP, wanda tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya lashe.

Kara karanta wannan

Tsohon ɗan takarar gwamna da wani babban jigon PDP sun sauya sheka zuwa NNPP mai kayan daɗi

Atiku Abubakar tare da Ayodele Fayose.
Da Dumi-Ɗumi: Fayose ya yi watsi da Atiku, ya ce wajibi mulki ya koma kudancin Najeriya a 2023 Hoto: sunnewsonline.com
Asali: UGC

A wani rubutu da ya saki shafinsa na Tuwita ranar Laraba, Fayose ya ce yanzu lokaci ne na kudancin Najeriya ya samar da shugaban ƙasa na gaba.

Tsohon gwamnan ya ce:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Kwansutushin ɗin PDP ya tanadi tsarin karba-karba a kujerar shugaban ƙasa. Sashi na 3 (c) ya tanadi cewa jam'iyya zata cika manufofinta ta hanyar tsayuwa kan tsarin karba-karɓa, yanki-yanki game da kujerun jam'iyya da na zaɓe don tabbatar da adalci da dai-daito."
"Shugaban ƙasa na yanzun ɗan arewa ne da zai kammala wa'adinsa biyu, hakan na nufin wajibi kujerar shugaban ƙasa ta koma kudanci a 2023 ko bakomai."

Akwai aiki a gaban PDP

Bayan zaɓen fidda gwani, babbar jam'iyyar hamayya PDP ta yi kira ga mambobinta masu ruwa da tsaki su maida wuƙar su kube, su haɗa kai don kwace mulki daga hannun APC a 2023.

Kara karanta wannan

An tsinci gawawwakin matasa 17 a gidan casu, Hukumar yan sanda

Sai dai, abubuwa sun dagulewa jam'iyyar PDP bayan zaɓen fidda gwanin, lokacin da Atiku Abubakar ya zaɓi gwamnan Delta, Ifeanyi Okowa, a matsayin abokin takararsa.

Ɗan takarar shugaban ƙasan ya zaɓi gwamna Okowa kan Wike duk da shawarin da wasu shugabannin PDP suka ba shi kan ya ɗauki gwamnan Ribas.

Jim kaɗan bayan faruwar haka, tsohon ministan harkokin Neja Delta, Goddsday Orubebe, ya fice daga jam'iyyar PDP.

A wani labarin kuma Hadimin gwamnan APC na jihar Imo ya yi murabus daga muƙaminsa, ya nemi a ba shi miliyan N77.2m

Wani rikici ya ɓarke a gwamnatin jihar Imo yayin da mai ba da shawari na musamman kan harkokin siyasa ga gwamna ya aje aikinsa.

Batos Nwadike, ya bayyana cew a ya ɗauki matakin ne bisa tilas saboda an watsar da ofishinsa ba'a tura masa kasafin kuɗi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel