Katsina: Masari ya sake nada kwamishinoninsa bayan sun sha kaye a zaben fidda gwani
- Gwamnan jihar Kastina ya daga wa majalisarsa kafa yayin da ya mayar dasu kujerunsu na da kafin yin murabus
- A baya, wasu daga majalisar kwamishinoni da fadar gwamnatinsa sun yi murabus domin tsayawa takarar wasu kujeru
- A wani jawabi da ya yi, gwamna Masari ya ce ba bukatar nemo wasu ko sake rantsar dasu, su ci gaba da aiki daga inda suka tsaya
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Katsina - Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya sake nada wasu daga cikin mambobin majalisarsa da suka ajiye mukamansu domin tsayawa takara a zaben fidda gwani na APC da aka gudanar kwanan nan.
Wadanda aka sake nadawa sun hada da kwamishinan kasafin kudi da tsare-tsare, Farouk Lawal Jobe, da takwaransa na raya karkara, Mustapha Mahmud, wadanda dukkansu suka tsaya neman tikitin takarar gwamnan jihar amma suka sha kaye.
Mataimakin gwamnan jihar, Mannir Yakubu, shi ma ya koma mukaminsa na kwamishinan noma, Daily Trust ta ruwaito.
Mai ba da shawara na musamman kan harkokin siyasa ga gwamna, Kabir Shaibu, wanda ya nemi tikitin takarar Sanatan Katsina ta tsakiya na daga cikin wadanda aka mayar, inji jaridar Today.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Hakazalika, da kuma mai ba da shawara na musamman kan bunkasa tattalin arziki, Abdulkadir Mamman Nasir, wanda ya nemi tikitin takarar majalisar wakilai ta mazabar Malumfashi/Kafur.
A jawabinsa, Masari ya ce:
“Suna nan a cikinmu a inda suke da. Don haka, muna jin abin da ya fi dacewa a yi shi ne mu nemi su dawo kuma sun amince su ci gaba daga inda suka tsaya.
“Tare da sabuwar dokar zabe, kowa na son sanin hannunsa. Na umurci sakataren gwamnatin jiha cewa mataimakin gwamna ya ci gaba da aikinsa na kwamishinan noma kuma ba ya bukatar a rantsar da shi”.
Zaben fidda gwanin APC: Yadda deliget 17 suka mayar min da kudi na, inji Sanata
A wani labarin, dan majalisa mai wakiltar yankin Kwara ta tsakiya, Sanata Ibrahim Oloriegbe, ya ce wasu deliget da ya ba da kudade a lokacin zaben fidda gwani na jam’iyyar sun mayar masa da abin sa.
Ya bayyana haka ne a lokacin da ya bayyana a gidan talabijin na Channels a shirin Sunrise Daily inda ya yi magana kan rikicin da ke cikin jam’iyyar mai mulki.
Sanata Oloriegbe ya caccaki tsarin da aka bi wajen gudanar da zabukan fidda gwanin da aka yi a wasu jihohin, inda ya zargi gwamnoni da kakaba deliget ga magoya bayan jam’iyyar, rahoton Leadership.
Asali: Legit.ng