Kungiyar Ma’aikata da ‘Yan kasuwan Najeriya sun tsaida ‘Dan takaran 2023 da za su zaba

Kungiyar Ma’aikata da ‘Yan kasuwan Najeriya sun tsaida ‘Dan takaran 2023 da za su zaba

  • Kungiyar kwadago da Kungiyar ‘Yan kasuwa su na tare da Jam’iyyar Labor Party a zabe mai zuwa
  • Shugabannin NLC da na TUC sun tabbatar da haka a wajen taron tunawa da Marigayi Pascal Bafyau
  • Ayuba Wabba ya ce wannan ne karon farko da ma’aikata za su goyi bayan ‘dan takaran LP a zabe

Abuja - Kungiyar kwadago ta Najeriya watau NLC, da takwararta TUC ta ‘yan kasuwa, za su marawa Peter Obi baya ne a zaben shugaban kasa na 2023.

Vanguard ta ce wadannan kungiyoyi sun sha alwashin nan a ranar Talata, 28 ga watan Yuni 2022.

Shugaban NLC na kasa, Ayuba Wabba da shugaban TUC, Quadri Olaleye sun yi alkawari sai inda karfinsu ya kare wajen ganin Peter Obi ya yi nasara a zaben.

Kara karanta wannan

2023: Kungiyar matasan APC sun dage, sun ce Zulum ne ya kamata ya yi takara da Tinubu

Wabba da Olaleye sun sha wannan alwashin a hedikwatar kwadago na Pascal Bafyau Labour da kuma sakatariyar TUC da suke babban birnin tarayya Abuja.

The Nation ta ce shugabannin kwadagon sun yi wa ma’aikata jawabi a jiya a wajen wata lacca ta musamman da aka yi domin a tuna da Marigayi Pascal Bafyau.

A jawabinsa, Wabba ya bayyana Peter Obi a matsayin lafiyayyen ‘dan takarar shugaban kasa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Peter Obi
‘Dan takaran LP, Peter Obi
Asali: Twitter

Shugaban kungiyar ta NLC ya ce Obi ne ‘dan takarar jam’iyyar LP na farko da ‘yan kwadago za su marawa baya a zaben shugaban kasa, ya ce za su tsaya masa.

An ji Wabba yana cewa ma’aikata sun fahimci yajin-aiki ba zai iya kawo karshen rashin adalcin da ake yi masu ba, a dalilin haka suka ga bukatar shiga siyasa.

Mun yi mubaya'a inji TUC

Kara karanta wannan

2023: Dattawan Kudu da Arewa za su fadi wanda ya kamata su zaba cikin 'Yan takara 7

Da yake na shi jawabin, Olaleye ya ce sun karbi Obi a matsayin ‘dan takarar da za su yi aiki da shi, kuma duk za su kada masa kuri’arsu a zaben shugaban kasa.

A cewar shugaban kungiyar ‘yan kasuwan, jam’iyyar Labour Party ta kara karfi domin babu gidan da babu ma’aikacin da yake karkashin TUC ko NLC a Najeriya.

Obi ya halarci taron da aka yi

Peter Obi ya samu kai wa duka wadannan kungiyoyi ziyara a hedikwatocinsu da ke garin Abuja.

‘Dan takaran ya ce ba kamfe ya kai shi ba, sai dai ya je domin amsa goron gayyatar da aka aika masa. A wurin, Obi ya yi bayanin yadda zai ceto tattalin arziki.

SMBLF ta kira taro a Abuja

Ku na da labari manyan Neja-Delta, Ohanaeze da Afenifere sun yi wani zama a garin Abuja, sun duba halin da kasa ta ke ciki da batun zaben shugaban kasa na 2023

Kara karanta wannan

Yau Kwankwaso zai yi zama na musamman da Nyesom Wike a kan shirin zaben 2023

Wadanda aka yi zaman da su sun kunshi Zamani Lekwot, Victor Attah, da Chukwuemeka Ezeife. Jagororin sun ce za su fadawa al'umma wanda za su kadawa kuri'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng