Za mu durkusa a gaban Wike idan hakan zai sa ya ci gaba da zama a PDP, in ji Walid Jibrin

Za mu durkusa a gaban Wike idan hakan zai sa ya ci gaba da zama a PDP, in ji Walid Jibrin

  • Shugaban kwamitin BoT na PDP, Walid Jibrin ya bayyana matakin da suke shirin dauka don hana Gwamna Nyesom Wike ficewa daga jam'iyyar
  • Jibrin ya ce koda za ta kama sai sun durkusa a gaban Wike ne kafin ya hakura da ci gaba da zama a jam'iyyar a shirye suke su aikata hakan
  • Ya kuma bayyana cewa suna shirin kafa kwamiti domin su je har inda gwamnan yake don tattaunawa da shi

Kaduna - Shugaban kwamitin amintattu na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Walid Jibrin, ya bayyana cewa jam’iyyar za ta yi duk abun da ya dace don tabbatar da ganin cewa gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike bai sauya sheka ba.

Jibrin ya bayyana hakan ne a ranar Litinin, 27 ga watan Yuni, yayin da yake jawabi ga manema labarai a jihar Kaduna, jaridar The Cable ta rahoto.

Kara karanta wannan

Mun Baka Awa 48: PDP Za Ta Yi Wa Obasanjo Fallasa Idan Bai Yi Karin Haske Kan Maganan Da Ya Yi Kan Atiku Ba

Nyesom Wike
Za mu durkusa a gaban Wike idan hakan zai sa ya ci gaba da zama a PDP, in ji Walid Jibrin Hoto: bbc.com
Asali: UGC

Wike ya yi takarar neman tikitin shugaban kasa na babbar jam’iyyar adawar kasar ta PDP amma ya sha kaye a hannun tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar a zaben fidda gwani.

Bayan zaben fidda gwanin wanda aka yi a watan Mayu, sai Wike ya zargi masu ruwa da tsaki daga yankin kudancin kasar da cin amana.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Hakazalika, da lokacin zabar dan takarar mataimakin shugaban kasa ya yi, Wike ne kan gaba a cikin mutane uku da aka gabatar amma sai Atiku ya zabi gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa a matsayin abokin takararsa.

Bayan wannan ci gaban, ana ta rade-radin cewa gwamnan na jihar Ribas na iya sauya sheka sannan kuma yan siyasa da dama daga jam’iyyun adawa ciki harda yan takarar shugaban kasa Peter Obi da Rabiu Kwankwaso suna ta kai masa ziyara.

Kara karanta wannan

An yi kus-kus: Abin da Bola Tinubu ya shaida wa sanatocin APC a wata ganawar sirri

Da yake magana kan kokarin tabbatar da ganin cewa jam’iyyar ta ci gaba da samun hadin kai gabannin babban zaben 2023, Jibrin ya ce za a kafa wani kwamitin sulhu domin ya ziyarci gwamnan na jihar Ribas.

Jibrin ya ce:

“Mun san yadda za mu magance matsalolinmu. Mun san cewa ba lallai ne gwamna Nyesom Wike ya yi farin ciki ba. Kudirin jam’iyyar ne kafa wani kwamitin sulhu da zai zauna da Wike don tattaunawa da shi, rokonsa sannan muna addu’a cewa ba zai bar jam’iyyarmu ba.”

Jibrin ya bayyana Wike a matsayin mutumin kwarai wanda ke ta yiwa jam’iyyar yaki kuma cewa jam’iyyar ba za ta so ganin komawarsa wata jam’iyya ba, rahoton Daily Post.

Ya kuma ce PDP za ta gana da dukkanin mutanen da suka yi takara a zaben fidda gwanin.

Ya ce:

“Duk za mu ziyarci Wike tare sannan idan za ta kama mu durkuwa Wike ne, za mu durkusa masa.

Kara karanta wannan

Jami'in INEC: Kuskure ne Ayyana Machina Matsayin 'Dan Takarar Sanatan Yobe ta Arewa a APC

“Muna ganin mutuncinsa. Muna daraja mutunci da gaskiyarsa wajen goyon bayan PDP. Mun yarda cewa a duk takara, dole a samu mai nasara da wanda zai sha kaye.”
Ya kuma shawarci mambobin jam’iyyar da su hada kai domin lashe zaben 2023, yana mai cewa PDP ta fadi zaben gwamnan da aka yi kwanan nan a jihar Ekiti saboda rashin hadin kai.
"Ina so in yi kira ga 'yan PDP da su yi aiki tare cikin hadin kai.
“Kada a raba kanmu. Dole ne mu hada kanmu. Idan muka fara samun matsala a tsakaninmu, da akwai karin matsaloli a gare mu.”

Peter Obi ya ziyarci Gwamna Nyesom Wike a Port Harcourt

A baya mun ji cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party (LP), Mista Peter Obi, ya ziyarci gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike a Port Harcourt a ranar Laraba, 22 ga watan Yuni.

Legit.ng ta tattaro cewa sun shafe tsawon awanni suna saka labule a tsakaninsu a gidan Gwamna Wike da ke Port Harcourt, babban birnin jihar Rivers.

Kara karanta wannan

2023: Zawarcin da APC, Peter Obi su ke yi wa Wike ya fara kada hantar jagororin PDP

Ana dai ta rade-radin cewa Wike na shirin ficewa daga jam’iyyar Peoples Democratic Party, PDP bayan ya fadi a zaben fidda gwanin jam’iyyar sannan kuma aka ki zabarsa a matsayin abokin takarar Atiku Abubakar, wanda zai daga tutar jam’iyyar a zaben shugaban kasa na 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng