Mu na tattaunawa da PDP da ‘Jam’iyyar kayan marmari’ inji ‘Danuwan Buhari, Hon. Fatihu

Mu na tattaunawa da PDP da ‘Jam’iyyar kayan marmari’ inji ‘Danuwan Buhari, Hon. Fatihu

  • Hon. Fatuhu Muhammad ya tabbatar da cewa magana tayi nisa tsakaninsa da jam’iyyun hamayya
  • ‘Dan Majalisar na Daura, Sandamu da Mai Adua ya na duba yiwuwar ficewa daga APC mai mulki
  • Muhammad yake cewa ‘yan jam’iyyar PDP da NNPP su na tuntubarsa domin sun san darajarsa a siyasa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Hon. Fatuhu Muhammad mai wakiltar mutanen Daura, Sandamu da Mai Adua a majalisar wakilan tarayya ya yi magana a kan batun sauya-sheka.

Da ya zanta da Daily Trust, Hon. Fatuhu Muhammad ya yi watsi da rade-radin da ke yawo na cewa har ya kai ga yin waje daga jam’iyyar APC mai rinjaye.

Amma duk da haka, ‘dan majalisar ya tabbatar da cewa yana magana da sauran jam’iyyun siyasa, kuma babu mamaki a ji labari ya sauya-sheka nan gaba.

Kara karanta wannan

Kwankwaso da Peter Obi su na tsere da INEC domin yi wa PDP da APC taron dangi mai-karfi

A cewarsa, ya na zantawa da jam’iyyun hamayya irinsu PDP da kuma NNPP, ya ce kowanensu ya na zawarcinsa, amma har yanzu bai tsaida matsaya ba.

Jawabin Fatuhu Muhammad

“Eh, ina tattauna sosai da PDP, magana ta yi nisa da jam’iyyar NNPP. Duk su na nema na;

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sun san abin da shiga ta jam’iyyarsu ta ke nufi, idan har APC ba ta san daraja ta ba. Ba da dadewa ba, zan dauki matsaya.”
Fatuhu Mohammed
Hon. Fatuhu Mohammed a Majalisa Hoto: @ahmad.ganga.545
Asali: Facebook

“Idan lokaci ya yi, zan sanar a Duniya, amma na fitar da jawabi bayan zaben fitar da gwani na cewa na kai korafin zaben.”
“Kwamitin sun kammala aikinsu, amma sai aka hada-kai da gwamnatin jiha, aka hana su gabatar da rahoton aikinsu.”
“Don haka ba su taimakawa tsarin. Wadanda ake taimako, su ne wadanda jam’iyya ta ke so, saboda haka mu na neman mafita.”

Kara karanta wannan

Labari mai dadi: Yajin-aikin Kungiyar ASUU ya kusa zama tsohon labari - Gwamnatin Buhari

Fatuhu Muhammad yake cewa jam’iyyarsa ta APC ta na jin tasirin rashinsa, don haka ta razana.

Dole sai da mu a Daura - Fatuhu

Jaridar ta kuma rahoto Honarabul Muhammad ya na bugun kirji, yana cewa a fadin mazabar Daura, babu wani abin da aka isa a yi a siyasa ba tare da shi ba.

Kawo yanzu ya ce bai yanke shawarar matsayar da zai dauka ba, ya ce da zarar ya yanke shawara, zai sanar da Duniya ko zai zauna, ko zai bar jam’iyyar.

NNPP ta nada jagorori a Katsina

Kwanakin baya aka ji Sanata Abdu Umar ‘Yandoma ya tabbatar da cewa an nada Alhaji Gambo Salisu a matsayin sabon shugaban NNPP na reshen jihar Katsina.

Alhaji Gambo Salisu, Hadi Maidawa Malumfashi, Dauda kurfi, Dauda kurfi, Abdulaziz Musawa, Hajiya Guye Daura su na cikin shugabannin jam'iyyar NNPP a jihar.

Kara karanta wannan

Majan LP da NNPP: Sai dai Peter ya zama mataimaki, Kwankwaso shugaba, inji NNPP

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng