AbdulMumini Jibrin ya daura hoton Kwankwaso ya 'badda kama, ya sha kayan Gayu

AbdulMumini Jibrin ya daura hoton Kwankwaso ya 'badda kama, ya sha kayan Gayu

  • Bayan komawa NNPP, AbdulMumini Jibrin ya koma goyon bayan Kwankwaso maimakon Tinubu
  • Jibrin ya siffanta Kwankwaso matsayin wani sabon guguwa da zai mamaye Arewa a zaben 2023
  • Abdul Mumini Jibrin na neman takarar kujeran dan majalisa mai wakiltar Kiru da Bebeji

Tamkar Barack Obama ko Donald Trump, dan takarar kujeran shugaban kasa a jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), Rabiu Musa Kwankwaso, ya sha kayan Turawa.

A hoton da aka daura a kafafen sadarwa, Kwankwaso ya sha farar yar riga don hoton yakin neman zabe.

Ba kasafai a kan ga Sanata Kwankwaso sanye da wata kaya sabanin babbar riga da jar hula ba.

Wannan sabon hoto da ya bayanna ya janyo cece-kuce a kafafen ra'ayi da sada zumunta.

Kara karanta wannan

APC ta nada Ganduje shugaban yakin neman zaben Gwamnan jihar Osun

AbdulMumimi Jibrin yace:

"Shugaban kasanmu Insha Allah, Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso. Sabon guguwan da zai mamaye Arewa a kayan gayu."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Asali: Legit.ng

Online view pixel