Takaitaccen tarihin mutum 7 da Buhari ya zaba domin su zama sababbin Ministocinsa
- A ranar Talata, 21 ga watan Yuni 2022, aka ji cewa Muhammadu Buhari ya aika sunayen Ministoci
- Idan an tabbatar da wadannan mutane bakwai, za su maye guraben Ministocin da suka ajiye aikinsu
- Sunayen wadanda aka aika sun hada da shugaban OGFZA da tsohon shugaban majalisa na jihar Imo
1. Henry Ikechukwu
Henry Ikechukwu ya rike Kwamishinan masana’antu a gwamnatin Okezie Ikpeazu. Daga baya ya fice daga PDP zuwa APC, ya nemi mataimakin shugaban jam’iyya.
Ikechukwu ya fito ne daga kauyen Ahuwa Oboro a garin Ikwuano, jihar Abia. ‘Dan siyasar ya yi sha’awar tsayawa takarar Sanatan Abia ta tsakiya a APC a zaben 2023.
2. Umana Okon Umana
Umana Okon Umana shi ne wanda ya yi wa APC takarar gwamnan Akwa Ibom a zaben 2015, amma ya sha kashi a hannun Udom Emmanuel da PDP ta tsaida.
Daga baya Muhammadu Buhari ya nada shi shugaban hukumar OGFZA mai kula da sha’anin harkar mai da gas. A 2019 aka kara masa wa’din shekaru uku.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
3. Umar Ibrahim El-Yakub
Hon. Umar Ibrahim El-Yakub shi ne Mai ba shugaban Najeriya shawara a kan harkokin majalisar wakilan tarayya tun bayan tafiyar Abdulrahman Kawu Sumaila.
Kafin yanzu Ibrahim El-Yakub ya taba zama ‘dan majalisar tarayya inda ya wakilci mazabar Birnin Kano da kewaye a jihar Kano daga shekarar 1999 zuwa 2007.

Asali: UGC
4. Goodluck Nanah Opiah
Rt. Hon. Chief Goodluck Nanah Opiah rikakken ‘dan siyasa ne wanda ya fito daga Abacheke Egbema, a 2007 ya zama shugaban majalisar dokokin jihar Imo.
Kafin yanzu Goodluck Opiah ya wakilci Ohaji/Egbema, Oguta, Oru a majalisar tarayya, shi ne Mai ba gwamna Hope Uzodinma shawara a kan harkar gas da mai.
5. Ekuma Joseph
Ekume Joseph shi ne wanda Mai girma Muhammadu Buhari ya zaba domin ya maye gurbin Ogbonnoya Onu daga jihar Ebonyi a majalisar FEC ta Ministoci.
Joseph ya taba zama Mai ba Gwamnan Ebonyi, David Umahi shawara na musamman. Daga baya aka nada shi a matsayin Kwamishina har zuwa Mayun 2021.
6. Ademola Adewole Adegorioye
Zaman Ademola Adewole Adegorioye Minista zai tabbatar da cewa Tayo Alasoadura ya yi biyu-babu bayan da ya ajiye kujerarsa, ya kuma rasa takarar Sanata a Ondo.
Legit.ng ta fahimci Ademola Adegorioye ya nemi zama 'dan majalisar tarayya na yankin Akure.
7. Odo Udi
Idan majalisa ta tantance Odo Udi, zai wakilci jihar Ribas a FEC. Zabinsa ya ba mutane mamaki domin ana tunanin Rotimi Amaechi ne zai sake komawa kujerarsa.
Udi ya rike shugaban karamar hukumar Abua Odua a Ribas a lokacin Amaechi yana Gwamna a 2008, ya kuma samu damar zarcewa a kan wannan kujera a 2011.

Kara karanta wannan
Shugaban kamfe ya kyankyasa inda Abokin takarar Tinubu zai fito daga Jam’iyyar APC
Abokin takarar Tinubu
Ku na da labari cewa wasu Matasa sun ba ‘Dan takaran APC, Asiwaju Bola Tinubu shawarar wanda ya kamata ya zama Mataimakinsa a zaben shugaban kasa.
'Yan North East All Progressive Congress Enlightenment Circle sun yi watsi da su Kashim Shettima da Gwamnoni masu-ci, sun bada sunan Abubakar Malami.
Asali: Legit.ng