Rikici ya kunnowa APC, ‘Yan adawa na iya karbe Jihar Shugaban kasa a zaben 2023

Rikici ya kunnowa APC, ‘Yan adawa na iya karbe Jihar Shugaban kasa a zaben 2023

  • Mutanen Mustapha Muhammad Inuwa ba su gamsu da zaben ‘dan takarar Gwamnan Katsina ba
  • Da alama ‘yan bangaren tsohon Sakataren gwamnatin jihar za su iya kawowa APC matsala a 2023
  • Shugabannin APC na jihar Katsina su na barazanar korar duk mai sukar takarar Dr. Dikko Radda

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Katsina - Wata sabuwar rigima ta kunno kai a jam’iyyar APC ta reshen jihar Katsina a sanadiyyar sakamakon zaben ‘dan takarar gwamna na 2023.

Jaridar nan ta Katsina Post ta rahoto cewa Dr. Mustapha Muhammad Inuwa ya fara babatu bayan ya rasa tikitin takarar gwamna a jam’iyyar APC.

Mustapha Muhammad Inuwa wanda ya sauka daga kan kujerar Sakataren gwamnatin jihar domin takara ya zargi ‘yan jam'iyya da cin amanarsa.

Rahoton da Daily Trust ta fitar a ranar Laraba ya tabbatar da cewa Mustapha Inuwa ya yi alkawarin taimakawa yaransa da suka shiga NNPP.

Kara karanta wannan

Abokin takara: Atiku na daf da daukar Gwamna mai-ci, Tinubu zai tafi da tsohon Gwamna

Wadanda suka sauya-shekar zuwa jam’iyya mai mulki zuwa NNPP su na zargin ba ayi masu adalci ba. Hakan na iya zama barazana ga APC a zabe.

Dr. Inuwa yake cewa an ki ba shi damar ya tsaya takarar gwamna a 2023 ne domin ba za a iya juya shi ba, sai aka zabi wani wanda bai san komai ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gwamna Masarida Dikko Radda
Gwamna Masari ya kai Dikko Radda wajen Shugaba Buhari Hoto: @dikko_radda
Asali: Twitter

Ko da bai ambaci suna ba, tsohon sakataren gwamnatin ya nuna sai yadda aka yi da wanda ya lashe zaben tsaida gwani a APC watau Dr. Dikko Radda.

Maslaha yana tare da Inuwa

Tsohon shugaban jam’iyyar APC na jihar Katsina, Shitu S. Shitu ya na cikin shugabannin APC da wasu manyan ‘yan siyasa da suka zauna da Dr. Inuwa.

Da yake magana a matsayin jigo a tafiyar Mustapha Inuwa, Shitu S. Shitu ya yi Allah-wadai da yadda zaben ‘dan takarar Gwamnan Katsina ya kasance.

Kara karanta wannan

2023: Watakila Bola Tinubu ya dauki Musulmi a ‘Dan takarar Mataimakin Shugaban kasa

Alhaji Shitu Maslaha yake cewa watakila Ubangiji ya yi nufin ya azabtar da jam’iyyar APC ne a Katsina don haka aka tsaida zakanya a maimakon zaki.

APC ta dauki zafi

Irin jawabin da aka rika yi a wajen taron ya fusata wasu ‘yan jam’iyya, inda aka ji mataimakin shugaban APC, Bala Habu Musawa ya na maida martani.

Bala Musawa ya fito yana barazanar cewa duk wani shugaba a APC na jihar Katsina da ya halarci taron da ake sukar ‘dan takaran na su zai bar jam’iyyar.

Da yake jawabi a Malumfashi, Musawa ya nemi duk wadanda ba su ji dadin nasarar Dr. Radda ba, da su yi hakuri ko dai su sauya-sheka daga APC mai mulki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel