Gwamnatin Zamfara Ta Bada Hutun Kwana 5 Don Yin Rajistan Zabe
- Gwamnan Jihar Zamfara Bello Matawalle na Jihar Zamfara ya bada hutun kwanaki biyar a jiharsa domin mutane su yi rajistan zabe
- Ibrahim Dosara, Kwamishinan Labarai na Jihar Zamfara ya ce hutun da gwamnatin ta bada zai fara ne daga ranar 20 zuwa 24 na watan Yuni
- Gwamnatin ta umurci kwamishinoni, mashawartan gwamna na musamman, shugabannin jam'iyya, masu rike da sarauta su saka idanu a yankunansu su tabbatar wadanda suka cancanci yin rajistan sun yi
Zamfara - Gwamna Matawalle na Jihar Zamfara ya ayyana ranar 20 zuwa 24 ga watan Yuni a matsayin ranakun hutun aiki domin bawa ma'aikatan gwamnati damar zuwa garuruwansu su yi rajista zabe su karbi katin PVC.
The Punch ta rahoto cewa hakan ne cikin wata takarda da Kwamishinan Labarai, Ibrahim Dosara, ya raba wa manema labarai a ranar Asabar.
Gwamnati ta umurci masu ruwa da tsaki su saka ido kan rajistan zaben a yankunansu
Kwamshinan ya ce:
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
"Da wannan sanarwar, dukkan kwamishinoni, mashawarta na musamman, sakatarorin dindindin, sauran manyan ma'aikatan gwamnati, jami'an jam'iyya da masu rike da sarauta su saka idanu kan aikin rajistan masu zaben da ake yi."
"An bada umurin hakan ne domin tabbatar da cewa dukkan wadanda suka cancanci yin zabe a gundumominsu da kananan hukumomi sun yi rajista, kuma sun karbi katinsu na zabe don su samu damar sauke nauyin da kasa ta daura musu."
Sanatan APC Ya Saka Wa Daliget Da Kujerun Hajji Bayan Sun Dawo Masa Da Kudinsa Don Ba Su Zabe Shi Ba
A wani rahoton, Sanata Smart Adeyemi wanda ya wakilci Kogi West a Majalisar Tarayya, ya bada kujerun Hajji ga mutum biyar cikin daligets din da ya bawa kudi amma ba su zabe shi ba a zaben fidda gwani na APC.
Adeyemi ya rasa damar komawa majalisar ne a yayin da ya samu kuri'u 43 a zaben fidda gwanin, hakan yasa ya zo na uku.
Sunday Karimi, wanda ya samu tikitin jam'iyyar ya samu kuri'u 288, yayin da Muyiwa Aina wanda ya zo na biyu ya samu kuri'u 73.
Asali: Legit.ng