Gwamnan Ekiti: Ba za mu karbi kudi ba, masu zabe sun dage, sun zargi APC da hauro da mutane don su yi zabe
- A yau Asabar, 18 ga watan Yuni, ne dubban jama'a suka fito domin zabar yan takarar da suke muradi a zaben gwamnan jihar Ekiti
- Sai dai an sha yar diyama a rumfar zabe ta 7, Ward 4, Ifaki, bayan mazauna yankin sun zargi mambobin APC da rabawa masu zabe kudi
- Mutanen sun fatattake su sannan suka tsaya tsayin daka cewa babu mai raba kudi a rumfar zaben
Ekiti - Yayin da zaben gwamnan jihar Ekiti ke gudana a yau Asabar, 18 ga watan Yuni, an sha yar dirama bayan mazauna yankin Ifaki sun zargi wasu mambobin APC da rabawa masu zabe kudi.
An gano mazauna yankin suna fatattakar wadanda ake zargi da rabon kudin a wajen faruwar lamarin a Ward 4, rumfar zabe ta 7, Ifaki.
Al’ummar yankin sun dage cewa lallai kada wanda ya raba kudi a rumfar zaben.
A wani lamarin, mazauna yankin sun zargi jam’iyyar APC da kawo yan kabilar Egbira garin domin su kada kuri’a.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) ce ta yi zargin.
Kai Tsaye: Yadda Ake Fafatawa a Zaben Gwamnan Jihar Ekiti
A gefe guda, Legit.ng Hausa ta kawo maku cewa a yau Asabar, sama da mutum 749,000 ne a jihar Ekiti za su yanke hukuncin wanda zai gaji Gwamna Kayode Fayemi a zaben da babu shakka za a matukar fafatawa.
Manyan masu taka rawar gani su ne Dr. Fayemi, gwamna mai ci yanzu da tsohon gwamnan jihar, Niyi Adebayo, wanda shi ne ke jagorantar kamfen din 'dan takarar APC, Biodun Oyebanji.
Wani tsohon gwamna, Ayodele Fayose, yana bangaren 'dan takarar PDP, Bisi Kolawole, yayin da 'dan takarar SDP, Segun Oni, shima tsohon gwamna ne.
Hakazalika, akwai 'yan takarar ADC, Wole Oluyede, wanda cikakken likita ne; na YPP shi ne Debo Ajayi da na ADP, Adeynka Alli, matashin ma'aikacin banki.
Asali: Legit.ng