Kai Tsaye: Sakamakon Zaben Gwamnan Jihar Ekiti sun fara fitowa

Kai Tsaye: Sakamakon Zaben Gwamnan Jihar Ekiti sun fara fitowa

A yau Asabar, sama da mutum 749,000 ne a jihar Ekiti za su yanke hukuncin wanda zai gaji Gwamna Kayode Fayemi a zaben da babu shakka za a matukar fafatawa.

A dukkan jam'iyyun siyasa 16 da suka tsayar da 'yan takara a zaben gwamnonin Ekiti, banda jam'iyyun APC, PDP da SDP, 'yan takarar sun ce nasara suka fito samu ba takara ba kawai.

Ku kasance tare da Legit.ng inda za ta ckawo muku labaran yadda ake fafatawa kai tsaye daga Ekiti.

APC ta bada ratar 60, 000

Abiodun Oyebanji, wanda ya tsayawa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a zaben jihar Ekiti ya tserewa abokin hamayyarsa da kuri’u 65,791.

Sakamakon kananan hukumomi 10 da aka fitar ya nuna Oyebanji yana da kuri’u 107,913, shi kuwa Segun Oni na jam’iyyar adawa ta SDP yana da 42,122.

Daily Trust ta ce jam’iyyar PDP ta bar mulki a shekarar 2019 ce ta uku a halin yanzu, ta samu 40,838.

APC ta ci kananan hukumomi 7, PDP 1, SDP 0

APC ta na da 7 LGAs

Kawo yanzu jam’iyyar APC ta tabbata wanda ta yi nasara a kananan hukumomin Ikere, Emure, Ekiti ta Kudu maso yamma, da Ekiti ta yamma.

Sauran kananan hukumomin jihar da Abiodun Oyebanji ya samu rinjaye a zaben sun hada da Oye, Irepodun/Ifelodun da karamar hukumar Ise/Orun.

‘Dan takaran PDP, Bisi Kolawole aka bada sanarwar ya yi nasara a karamar hukumar Efon Alaye, Segun Oni na SDP bai da karamar hukuma ko daya.

SDP ta sha kashi a garin Obi

Rahoton da Legit.ng ta samu ya tabbatar da Biodun Oyebanji ne ya samu kuri’u mafi yawa a karamar hukumar Ido-Osi inda Segun Oni na SDP ya fito.

APC: 10,321

PDP: 2,871

SDP: 9,489

LP: 10

Sakamakon Zaben Kananan Hukomomi sun fara bayyana

Karamar hukumar Ido-Osi

APC: 10,321

PDP: 2,871

SDP: 9,489

LP: 10

Karamar hukumar IREPODUN/IFELODUN

APC: 13,125

PDP: 4712

SDP: 5010

Karamar Hukumar Efon

ADP-77

APC-4012

PDP-6303

PRP-20

SDP-339

Karamar Hukumar Ekiti ta yamma

APC: 15322

PDP: 3386

SDP: 3863

Karamar hukumar Ekiti ta Kudu maso Yamma

APC - 9,679

PDP - 4,474

SDP - 4577

Karamar hukumar Oye

APC - 13,396

PDP - 4,122

SDP - 5,391

Karamar hukumar Emure

APC – 7,728

PDP - 2,610

SDP - 3,445

PU 10, Ward 5, Emure LGA

A-0

AAC-0

ADC-6

ADP-14

APC-722

APGA-3

APM-2

APP-12

LP-2

NNPP-4

NRM-1

PDP-216

PRP-02

Sdp- 452

YPP-9

ZLP-5

Sakamakon zaben karamar hukuma Ekiti ta Kudu maso Yamma, Ilawe ta 1

Karamar hukumar Ekiti ta Kudu maso Yamma, Ilawe ta 1

Masu rijistar zabe- 3786

An Tantance - 1550

A- 0

AAC - 01

ADC - 07

ADP - 18

APC - 824

APGA- 01

APM- 0

APP- 11

LP - 0

NNPP - 04

NRM - 02

PDP- 218

PRP- 02

SDP- 400

YPP- 02

ZLP- 02

Sakamakon zaben karamar hukumar Ise Orun, gunduma ta 2

Karamar hukumar Iṣẹ/Orun, gunduma ta 2- Oso Ise 2

Jma'ar dake da ijistar zabe 5156

An tantance mutum 2030

A- 0

AAC- 3

ADC- 4

ADP- 16

APC- 968

APGA- 1

APM- 1

APP- 16

LP- 0

NNPP- 4

NRM- 1

PDP- 292

PRP- 2

SDP- 679

YPP- 6

ZLP- 3

Ekiti South West LGA, Ilawe 5

APC - 640

PDP- 194

SDP- 387

Ekiti West Ward 6, PU 003

A- 0

AAC- 0

ADC-0

ADP-0

APC-296

APGA- 0

APM- 0

APP-0

LP-0

NNPP-0

NRM-0

PDP- 2

PRP-0

SDP-0

YPP-0

ZLP-0

PU 020, Ward 10, Irepodun/Ifelodun LG

PU 008, Ward 4, Moba LGA

APC: 110

PDP: 41

SDP: 86

PU 007, Ward 3, Moba LG

APC: 163

PDP:38

SDP: 122

PU7, ward 7, Omuo-Ekiti, Ekiti-east LGA

SDP: 46

PDP: 110

APC: 141

PU006, Ward 2, Ilejemeje LG

ADP: 3

PDP: 10

APC: 93

ADC: 17

SDP: 51

PU01, Ward 4, Ijigbo, Ado-Ekiti LG

APC: 188

PDP: 71

SDP: 244

Sakamakon zabe

Ademilua compound, PU 006, Ward 06, Ikogosi, Ekiti West.:

APC: 169

PDP: 0

SDP: 7

NNPP: 1

PU006 Oye II, Oye LG.

APC: 41

PDP: 13

SDP: 35

PU017, Oye II, Oye LG

APC: 69

SDP: 42

PDP: 7

Filin Makaranta Ta Musamman Ta Makafi, Akwatin Zabe, PU 008, Gundumar Oke Osun Ta 6:

ADC: 09

ADP: 00

APC: 072

PDP: 06

SDP: 040

PU 10, Ward A, Ijero-Ekiti

APC: 37

PDP: 12

SDP: 11

PU 002, Ward 2, Ido Osi

SDP: 185

APC: 21

PDP: 1

PU: 008 Makarantar Firamare ta St Mary, ODE 11 Area (gunduma ta 3), Karamar hukumar Gbonyin

PDP 58

APC 71

SDP 77

PU 003, Kofar gidan Alamo ‐ ILAMO (Code 02), Karamar Hukumar Ikole Ekiti

An tantance 213

Masu kada kuri'a da suka yi rijista 559

APC 103

PDP 78

SDP 19

Ward 10 Unit 7 Ado ‘J’ Okesa

PDP 24

SDP 59

APC 135

Ward:07, Unit:07, Wesley United Primary School Ekiti East Local Government

SDP -46

APC -141

PDP -110

Bidiyon wakilan Jam'iyya suna bawa hammata iska a mazabar Fayose

Wasu wakilan jam'iyya (wato agent) sun bawa hammata iska a wurin zabe a mazabar tsohon gwamnan Jihar Ekiti Ayodele Fayose.

Kamar yake a bidiyon, mutane suna kokarin raba su yayin da suke kokarin kada juna.

Biodun Oyebanji yana zaga wa rumfunan zabe tare da matarsa

Dan takarar gwamna na jam'iyyar APC a zaben na Ekiti, Biodun Oyebanji, a halin yanzu yana zaga wa rumfunan zabe tare da matarsa.

Ana tantance masu zabe tare da jefa kuri'a a karamar hukumar Emure

Zabe na tafiya yadda ya kamata a karamar hukumar Emure, Gunduma ta 5, rumfar zabe ta 10.

Na'urorin tantance masu zabe suna aiki ba matsala a lokacin wallafa wannan rahoton.

Ina da tabbacin nine zan lashe zabe – Oyebanji

Dan takarar gwamna na jam’iyyar APC, Biodun Oyebanji, ya nuna karfin gwiwar cewa shine zai lashe zaben na jihar Ekiti wanda ke kan gudana a yanzu haka.

Oyebanji ya bayyana hakan ne bayan ya kada kuri’arsa.

Bidiyon tsohuwa mai shekaru 105 tana kwasar rawa bayan kada kuri'a

A rumfar zabe mai lamba 006 dake Ofaki a karamar hukumar Ido-Osi ta jihar Ekiti, wata tsohuwa mai shekaru 105 ta kwashi rawa bayan ta kada kuri'a cike da farin ciki.

Ekiti jihar Farfesoshi ce, ba za mu karba cin hanci ba, Masu Kada Kuri'a

Yayin da ake tsaka da kada kuri'u a rumfunan zabe a jihar ekiti, wasu masu kada kuri'a sun tabbatar da cewa ba za su karba cin hanci ba.

A cewarsu, jihar Ekiti jiha ce ta fafesoshi ba jahilai ba. Don haka babu ruwansu da rashawa.

Dan takarar PDP, Bisi Kolawole, ya kada kuri’arsa

Dan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party, Bisi Kolawole, ya kada kuri’arsa a mazabarsa ta 001, Ward 8, Efon VIII, Ojodi 1, jaridar Punch ta rahoto.

Bisi Kolawole
Kai Tsaye: Yadda Ake Fafatawa a Zaben Gwamnan Jihar Ekiti Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

Gwamna Kayode Fayemi ya isa mazabarsa domin kada kuri’a

Gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi, ya isa mazabarsa domin kada kuri’arsa a zaben gwamnan jihar da ke gudana a yanzu haka.

Masu zabe sun fara fita rumfunar zabensu domin ganin ba a barsu a baya ba

A rumfar zabe ta 003, ward 06, Ikogosi, Ekiti ta yamma, an gano masu zabe zaune suna jiran jami’an zaben su bayar da umurnin fara shirin.

Hakazalika a rumfa ta 10, ward 4, Ijigbo, Ado Ekiti, an gano wasu dattawa mata da suka fito don kada kuri’a.

A cewarsu:

“Mun rigada mun ga sunayenmu a cikin jerin wadanda za su kada kuri’a. mun shirya sauke hakkin mu na zabar wanda muke muradi.”

An fara tantance masu zabe da kada kuri'a a karamar hukumar Ado

An fara tantance masu zabe da kada kuri misalin karfe 8.30 na safe a rumfar zabe ta 002, gunduma ta 10, karamar hukumar Ado.

INEC ta sanar da lokacin fara zabe da kuma lokacin kammalawa

Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta ta bayyana cewa za a fara tantance masu zabe da kada kuri’a da misalin karfe 8:30 na safe sannan a rufe da karfe 2:30 na rana.

Kamar yadda ta wallafa a shafinta na Twitter, INEC ta ce duk mai rijistan zabe da ya shiga layi kafin karfe 2:30 na rana za a tantance shi don ya kada kuri’a, amma duk wanda ya zo bayan 2:30 na rana ba za a bari ya shiga layin ba.

An rarraba jami'an INEC zuwa rumfunan zabe

An rarrabe jami'an INEC tare da kayan aikinsu zuwa rumfunan zabe a kananan hukumomin Ikole ta Yamma, Ijero da Irepodun/Ifelodun da karfe 6:30 na safiyar yau.

An tsaurara matakan tsaro a fadin jihar

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa an tsaurara matakan tsaro a jihar ta Ekiti yayin da jam’iyyun siyasa ke fafatawa wajen neman kuri’u a zaben gwamnan da za a yi.

Yan takarar gwamnan Ekiti
Kai Tsaye: Yadda Ake Fafatawa a Zaben Gwamnan Jihar Ekiti Hoto: Segun Oni
Asali: UGC

Online view pixel