Mu na tattaunawa da su Peter Obi - Kwankwaso ya tabbatar da shirin taron dangi a 2023

Mu na tattaunawa da su Peter Obi - Kwankwaso ya tabbatar da shirin taron dangi a 2023

  • Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya tabbatar da cewa su na kan tattaunawa da 'yan jam’iyyar LP
  • Akwai yiwuwar ‘Dan takarar shugaban kasan na jamiyyar NNPP ya hade da su Peter Obi a 2023
  • Hakan ta sa duk Jam’iyyun ba su fitar da asalin ‘yan takararsu na mataimakin shugaban kasa ba

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - ‘Dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar hamayya ta NNPP, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ya zanta da manema labarai a kan shirin 2023.

A wasu hira da aka yi da shi a gidajen rediyon BBC Hausa da VOA Hausa, Rabiu Musa Kwankwaso ya shaida cewa su na ta tattaunawa da bangaren Peter Obi.

Kamar yadda mu ka samu labari a safiyar Asabar, 18 ga watan Yuni 2022, Sanata Rabiu Kwankwaso yana kokarin ganin yadda za a bullowa 2023.

Kara karanta wannan

Kwankwaso: Na tabbata Zan Yi Nasara, Ba Zan Janye Wa Atiku Ko Tinubu Ba

Wani Hadimin tsohon gwamnan na jihar Kano, Saifullahi Muhammad Hassan ya tabbatar da wannan magana a shafinsa na Facebook a daren na Asabar.

A gajeren jawabin da ya fitar, Saifullahi Muhammad Hassan bai yi wani karin-haske ba, sai dai kurum ya tabbatar da rade-radin da ke ta faman yawo a gari.

Abokin takara na wucin-gadi

A tattaunawarsa da VOA Hausa, Kwankwaso ya ce tuni jam’iyyar NNPP ta bada sunan abokin takararsa a zaben 2023, amma wanda aka zaba na wucin-gadi ne.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwankwaso
Rabiu Kwankwaso tare da jama'a a Abuja Hoto: @SaifullahiMohHassan
Asali: Facebook

Ana sa ran idan tattaunawar da NNPP da take yi da sauran jam’iyyu ta kammala, jam’iyyar za ta bada sunayen wadanda za su yi mata takara a zaben na badi.

Da ya zanta da BBC, Kwankwaso yace ba a gama magana ba, kuma bai fito karara ya fadi wanda zai yi takarar shugaban kasa da wanda zai yi na mataimaki ba.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Atiku yana ruwa, magoya bayan Wike su na barazana a kan dauko Okowa

Sai dai tsohon Gwamnan ya nuna za a duba matsayi wajen zaben wanda ya fi dacewa da takara.

Rataya aka ba ni - Doyin Okupe

A daren nan aka ji Doyin Okupe wanda shi ne wanda jam’iyyar LP ta bada sunansa a matsayin abokin takarar Peter Obi, yana bayanin halin da ake ciki.

Dr. Doyin Okupe ya fadakar da magoya bayansu cewa an mikawa INEC sunansa ne kurum saboda gudun wa’adin da aka ba jam’iyyu ya wuce a ranar Juma’a.

Darekta Janar din na yakin neman zaben Obi ya ce wannan mataki da aka dauka zai bada dama a karkare maganar taron dangin da kananan jam’iyyu ke yi.

Kamar yadda Kwankwaso ya fada, Okupe ya ce idan abubuwa sun tabbata, LP za ta fitar da ‘yan takara.

Atiku yana ruwa a PDP - Yaran Wike

Biyo bayan ba Ifeanyi Okowa takarar mataimakin shugaban kasa a PDP, an ji labari jiga-jigan jam'iyya sun ce Atiku Abubakar ya saurari sakamakon zabe.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Atiku ya shiga ganawa da Gwamnonin PDP kan zabo abokin takararsa

Wani shugaban karamar hukuma a Ribas ya ce Atiku ya sabawa abin da jam’iyya ta ce, wani na-kusa da Nyesom Wike ya ce ana neman yakar ubangidansu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng