Tikitin Musulmi-Musulmi: Kiristoci na da kariya saboda matar Tinubu fasto ce, inji Orji Kalu
- Tsohon gwamnan jihar Abia, Orji Kalu ya tofa albarkacin bakinsa kan tsarin da APC ta ke so ta bi na tsayar da Musulmi da Musulmi a matsayin shugaban kasa da mataimakin shugaban kasa
- Shugaban masu tsawatarwar a majalisar dattawa, ya ce kada kiristoci su ji tsoro koda anyi Musulmi da Musulmi domin matar Bola Tinubu Fasto ce
- Ya ce ko shakka babu uwargidar Tinubu wacce ke da ilimin siyasa za ta tsaya masu kasancewarta kirista kuma fasto
Abuja - Shugaban masu tsawatarwa a majalisar dattawan Najeriya, Sanata Orji Uzor Kalu, ya tsoma baki a cece-kuce da ake ta yi kan batun tsayar da dan takarar shugaban kasa da mataimakinsa daga addini guda.
Ana dai ta kai ruwa rana tun bayan da alamu suka nuna jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki na iya tsayar da Musulmi da Musulmi a matsayin yan takararta na kujerar shugabancin kasar.
Yayin da kungiyar kiristocin Najeriya ta yi watsi da shawarar sannan ta gargadi jam’iyyu a kan haka, wasu masu ruwa da tsaki sun bukaci yan Najeriya da su mayar da hankali kan cancanta fiye da akida.
Da yake jawabi ga manema labarai a majalisar dokokin tarayya a ranar Laraba, Orji Kalu ya bukaci kiristoci da kada su ji tsoro tunda matar Asiwaju Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa a jam’iyya mai mulki, Fasto ce, Daily Trust ta rahoto.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Jaridar Vanguard ta nakalto Kalu yana cewa:
“Bari na fada maku, a gidana, matata ce jagorar gida a zahirin gaskiya. Ko ku mazan da ke nan, yanzu da matanku basa nan, sune kan gida. Kamar idan na sanya wannan tufafin, matata za ta ce mun ‘mai gidana, wannan tufafin bai yi ba ka cire shi’. Matarka za ta fada maka Kosai da kunu ya kamata ka sha, ko za ka yi jayayya da ita, sai ka sha wannan kunun kuma matarka na so ka biya kudin makarantar yara, ko ka yi jayayya ko baka yi ba, sai ka biya kudin nan.
“Kiristoci su sanya ransu a inuwa saboda matar Tinubu Fasto ce kuma tunda fasto ce toh muna da kariya saboda ba matar gida bace. Tana da ilimin siyasa.”
Matar Tinubu, wacce a halin yanzu ke wakiltar Legas ta Tsakiya a Majalisar Dattawa, an nada ta a matsayin mataimakiyar Fasto na Redeemed Christian Church of God (RCCG) a 2018.
Legit.ng Hausa ta nemi jin ta bakin Mallam Muhammad Auwal, wani marubuci mai zaman kansa, kan tasirin da ke tattare da Tinubu ya dauki Musulmi dan arewa domin su yi takara tare inda yace:
“Idan aka yi duba da kundin tsarin mulki, yace sai ɗan takarar shugabancin ƙasa ya samu kaso 25 na ƙuri'un da aka kaɗa a jahohi 2 bisa 3 na Najeriya. Anan ana maganan kaso 25 na ƙuri'un aƙalla jahohi 25 kenan.
“A maslahan cin zaɓe na Tinubu, dole sai mataimakinsa ya zama Musulmi ɗan Arewa ne zai iya samun kaso mafi tsoka daga jahohin Arewa maso yamma da suka haɗa da Kaduna, Kano, Katsina Jigawa, Zamfara, Sakkwato da Kebbi. Kuma su ne jahohin da suka fi yawan ƙuri'u idan ka haɗasu da Borno da Legas, dukkanin jahohi 8 na APC ne!
Ba Mu Yarda Da Musulmi 2 Ba: Kungiya Ta Bayyana Kirista Da Yafi Dace Wa Tinubu Ya Dauka a Matsayin Mataimaki a 2023
“Haka zalika Arewa maso gabas da ta haɗa da Borno, Yobe, Gombe, Taraba, Adamawa da Bauchi, APC na da 3, PDP na da 3, koda yake nan ne yankin Atiku, amma APC za ta samu ƙuri'un da take buƙata.
“Arewa ta tsakiya kuwa (Neja, Nassarawa, Kwara, Kogi, Benuwe da Filato) APC na da 5, PDP na da 1, za a iya raba ƙuri'u anan saboda duk da jahohi ne na APC, amma akwai Kiristoci da yawa a yankin wanda zasu ma APC bore.
“A yankin kudu maso yamma kuwa, yankin da Tinubu ya fito, akwai jahohi 6, guda 5 APC ke mulka yayin da PDP ke da ɗaya tal! Cinye du Tinubu zai ma ƙuri'un yankin nan sakamakon Yarbawa na ganin lokacinsu na sake ɗarewa karagar shugabancin Najeriya ne, kuma sun fi fifita ƙabilanci akan addini.”
Babagana Kingibe ya aika sunayen mutum 3 ga Tinubu ya zabi abokin takara harda tsohuwar minista ciki
A wani labarin, mun ji cewa tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babagana Kingibe, ya mika wa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Tinubu, sunayen mutane uku don ya zabi abokin takara a cikinsu.
Kingibe wanda ya kasance abokin takarar marigayi MKO Abiola a zaben shugaban kasa na ranar 12 ga watan Yuni 1993, ya mika sunayen ga gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu, don ya gabatarwa Tinubu domin a tantance.
Kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto, jerin sunayen na dauke da sunan: Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, Mataimakiyar babban sakataren gwamnatin tarayya, Amina J. Mohammed da Jami’in hulda da jama’a na majalisar dokokin kasar a lokacin mulkin Olusegun Obasanjo na farko, Kashim Ibrahim-Imam.
Asali: Legit.ng