An bukaci Atiku, Tinubu, Kwankwaso da ‘Yan takara su bayyana dukiyar da suka mallaka

An bukaci Atiku, Tinubu, Kwankwaso da ‘Yan takara su bayyana dukiyar da suka mallaka

  • Socio-Economic Rights And Accountability Project ta na so a san sirrin aljihun masu neman takara
  • Kungiyar SERAP ta bukaci ‘yan takarar shugaban kasa su sanar da Duniya abin da suka mallaka
  • Prince Adewole Adebayo wanda yake takara a jam’iyyar SDP ne kurum ya iya bayyana kadarorinsa

Abuja - Kungiyar Socio-Economic Rights And Accountability Project (SERAP) ta kalubalanci ‘yan takarar shugaban kasa su bayyana duk kadarorinsu.

Sun ta ce kungiyar ta SERAP ta na so masu neman kujerar shugaban kasa a zaben 2023 su fadawa Duniya sirrin kudi da duk kadarorin da suka mallaka.

A cewar kungiyar, Prince Adewole Adebayo wanda yake neman takara a jam’iyyar SDP ne kurum ya iya bayyana abin da ya mallaka har zuwa yanzu.

Prince Adewole Adebayo wanda ya mallaki gidan talabijin na Kaftan ya nuna ya mallaki wata cibiyar nazari wanda ke hada magungunan cutar sikila.

Kara karanta wannan

Kusoshi a Jam’iyya sun dage Tinubu ya dauki Mataimaki daga mutum 2 a Gwamnatin Buhari

Har ila yau, ‘dan takaran ya ce yana samun kudi da wannan cibiya da kuma harkar noma da yake yi.

Sauran manyan ‘yan takaran irinsu Bola Tinubu na APC da Atiku Abubakar na PDP, Rabiu Kwankwaso da Peter Obi ba su kai ga yin koyi da Adebayor ba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Atiku Abubakar
Wazirin Adamawa, Atiku Abubakar Hoto: Atiku.org
Asali: Facebook

Me dokar kasa ta ce?

Legit.ng Hausa ta fahimci babu wata doka a kundin tsarin mulkin Najeriya da ta wajabtawa masu neman takara bayyana kadarorinsu kafin su iya shiga zabe.

Amma SERAP ta bakin mataimakin darektanta, Kolawole Oluwadare, ya ce yin hakan zai taimaka wajen tabbatar da gaskiya idan ‘yan takaran sun shiga ofis.

Oluwadare yake cewa akwai bukatar masu kada kuri’a su san abin da ‘yan takara za su yi kan harkar kare hakkin Bil Adama da bin doka idan sun yi nasara.

Kara karanta wannan

Burin Atiku a zaben 2023: Ina sa ran 'yan Najeriya za su yi kasa-kasa da jam'iyyar APC

Sayen kuri’un talakawa

Rahoton da Punch ta fitar a karshen makon jiya ya nuna cewa kungiyar mai zaman kanta, ta yi kira ga ‘yan takaran da su gujewa sayen kuri’un masu yin zabe.

SERAP ta ke cewa dole a gujewa sayen kuri’u kafin zabe da kuma lokacin da ake kada kuri’a.

PDP za ta ci zabe - Dino

A jiya ne aka labari tsohon Sanatan jihar Kogi, Dino Melaye ya jero abubuwan da suka sa 'dan takaran PDP, Atiku Abubakar ya sha gaban Asiwaju Bola Tinubu.

Sanata Melaya ya ce ‘Dan takararsu zai doke jam'iyyar APC domin ya fi Tinubu shahara, kwarewa a siyasa, gogewa a aiki, sanin matsalolin Najeriya, da lafiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel