Ekiti 2022: 'Idan Ba Kuri'a, Ba Kudi', Bidiyon Tinubu Yana Yi Wa Masu Zabe Ba'a a Wurin Kamfen
- Asiwaju Ahmed Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC a zaben shekarar 2023 ya fada wa mutane 'sai sun yi zabe za su samu kudi'
- Tinubu, ya yi wa dandazon magaya bayan jam'iyyar ta APC mai mulki wannan ba'ar ne a Jihar Ekiti a wurin yakin neman zaben gwamna na Biodun Oyebanji a zaben gwamna da ke tafe a jihar
- Baya ga Tinubu, wasu jiga-jigan jam'iyyar APC da suka hallarci wurin kamfen din sun hada da Gwamna Kayode Fayemi na Jihar Ekiti da takwararsa na Jihar Ogun, Dapo Abiodun da saura
Jihar Ekiti - Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress, APC, a zaben 2023, Asiwaju Bola Tinubu, ya bukaci al'ummar Jihar Ekiti su fito su yi zabe idan ba hakan ba ba za a biya su ba.
Tinubu, wanda ya ziyarci a Jihar Ekiti a ranar Talata ya furta hakan ne wurin yakin neman zabe na dan takarar gwamna na jam'iyyar, Biodun Oyebanji gabanin zaben da ake shirin yi ranar Asabar 18 ga watan Yunin 2022.
Ya kuma kambama kansa cewa bai taba fadi zabe ba a baya.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Tinubu ya ce:
"Ban taba shan kaye a zabe ba a baya."
Yayin da ya ke magana da harshen yarbanci, jagoran na APC na kasa, ya ce :
“To ba t’eka, o le te owo” ma'ana, “idan ba ka yi zabe ba, ba za ka iya rike kudi ba.”
Tinubu ya kuma ce "jam'iyyar Peoples Democratic Party, jam'iyyar ce mai kara talauci," yana mai kira ga mutanen jihar su zabi APC a matakin jiha da kasa a zaben shugaban kasa na 2023.
Sauran jiga-jigan jam'iyyar APC a wurin kamfen din sun hada da Gwamna Kayode Fayemi na Jihar Ekiti da takwararsa na Jihar Ogun, Dapo Abiodun da wasu.
Ga bidiyon a kasa:
Ba Mu Yarda Da Musulmi 2 Ba: Kungiya Ta Bayyana Kirista Da Ya Dace Tinubu Ya Dauka a Matsayin Mataimaki a 2023
A wani rahoton, Kungiyar matasan Kudu da Arewa, 'The Southern-Northern Progressive Youth Congress' ta soki shirin da ake hasashen jam'iyyar APC na yi na zabarwa dan takararta, Asiwaju Bola Tinubu, wani musulmi a matsayin mataimaki a zaben 2023.
Kungiyar cikin sanarwar da ta fitar mai dauke da sa hannun shugabanta na kasa, Nsebabi Brownson da Sakatarenta Bashir Aliyu Galadanci, sun goyi bayan a zabi Sakataren Gwamnatin Tarayya, SGF, Boss Mustapha a matsayin mataimakin Tinubu, rahoton Leadership.
Asali: Legit.ng