Tinubu ba sa’an Atiku ba ne, kafin 12:00 PDP ta kai APC kasa, Dino Melaye ya jero dalilansa

Tinubu ba sa’an Atiku ba ne, kafin 12:00 PDP ta kai APC kasa, Dino Melaye ya jero dalilansa

  • Sanata Dino Melaye ya yi kurin cewa tun kafin rana ta gama kai tsakiya, PDP za ta lashe zaben 2023
  • Tsohon Sanatan jihar Kogi ta yamma yace Atiku Abubakar ya sha gaban Asiwaju Bola Tinubu na APC
  • Dino Melaye ya yi ikirarin Bola Tinubu bai da koshin lafiya, don haka ma bai dace da hawa mulki ba

Abuja - Tsohon Sanatan jihar Kogi, Dino Melaye ya yi wata hira da gidan talabijin na Channels, inda aka yi magana da shi a kan sha’anin siyasar kasa.

Sanata Dino Melaye ya nuna babu abin da zai hana ‘dan takarar jam’iyyarsu ta PDP, Atiku Abubakar doke Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC.

Dino Melaye ya ce a mizanin siyasa, ‘dan takaran da APC ta tsaida watau Bola Ahmed Tinubu tamkar jariri ne idan aka kamanta shi da Atiku Abubakar.

Kara karanta wannan

Abokin takara: Atiku na daf da daukar Gwamna mai-ci, Tinubu zai tafi da tsohon Gwamna

Da mu ka bibiyi hirar, mun ji Melaye yana cewa sun ba Atiku shawarar ya tanadi jawabin murnar lashe zabe, domin shi za a rantsar a kan mulki a 2023.

“Idan ana maganar shahara a siyasa, Bola Tinubu da Atiku Abubakar ba tsaran juna ba. Ta ina Tinubu zai sha gaban Atiku?
“Ya motar Volkswagen za ta fi karfin 9/11? Idan ana maganar kwarewa a siyasa, Atiku da Bola Tinubu ba warin juna ba ne?

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dino Melaye
Sanata Dino Melaye da Atiku Abubakar Hoto: Dino Melaye
Asali: Facebook

“Atiku ya janyewa MKO Abiola takara…Atiku Abubakar ya yi mataimakin shugaban kasa, ya fi Tinubu gogewar sanin aiki.”

- Sanata Dino Melaye

A hirar da aka yi da shi, Dino Melaye ya kuma yi ikirarin babu wanda ya lakanci matsalolin da suka dabaibaye Najeriya a yau irin ‘dan takararsu na PDP.

Melaye ya ce idan ana maganar sanin mutane, karfi a siyasa da fahimtar Najeriya, Atiku ne a gaba, don haka cikin sauki zai lashe zaben shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Ciki ya duri ruwa: Mun ji tsoron Bola Tinubu ya samu takara a APC inji ‘Dan takaran PDP

Tinubu bai da lafiya - Dino

Har ila yau, Melaye wanda ya wakilci Kogi ta yamma a majalisar dattawa ya ce Bola Tinubu bai da isasshen lafiya da kwarin da zai shugabanci kasar nan.

Sanatan yake cewa a doka, ba zai yiwu a samu shugaban da ba zai iya aiki ba, yace a rubuta da babban baki, zuwa 12:00 na rana, PDP ta tika Tinubu da kasa.

Abokan takarar Atiku da Tinubu

Dazu kun ji labari Babagana Kingibe ya bada shawarar Bola Tinubu ya dauki dauki Babagana Zulum ko Amina J. Mohammed a matsayin mataimakinsa.

Janar Aliyu Gusau da ‘yan kwamitinsa su na so Atiku Abubakar ya tsaya a kan Ifeanyi Okowa da wasu Gwamnoni biyu duk daga yankin kudancin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel