El-Rufai, Zulum, Boss da ‘Yan siyasan Arewa 8 da a cikinsu za a nemi Mataimakin Tinubu
- Abin da ya ragewa jam’iyyar APC shi ne fito da ‘dan takarar kujerar mataimakin shugaban kasa
- Ciwon kan Asiwaju Bola Tinubu bayan lashe tikitin APC shi ne zaben wanda zai nemi mataimaki
- Ana tunanin Bola Tinubu zai dauko abokin takararsa ne daga cikin gwamnonin jihohi masu-ci a yau
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
A wani rahoto da ya fito daga Arise TV, akwai gwamnonin jihohin Arewa da manyan ‘yan siyasa da jami’an gwamnati da ake tunanin su na harin tikitin.
Ga jerin su nan kamar haka:
1. Atiku Abubakar Bagudu
Na farko a jerin shi ne Sanata Atiku Abubakar Bagudu. Gwamnan Kebbi shi yake rike da kujerar shugaban gwamnonin APC na kasa, don haka yake da dama.
2. Nasir El-Rufai
Ana kawo Gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai a wannan jeri. Gwamnan ya tsaya tsayin-daka wajen ganin an ba ‘Yan kudu takara a zabe mai zuwa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
3. Abdulahi Umar Ganduje
Daga cikin wadanda suka dade su na goyon bayan Bola Tinubu akwai Abdullahi Umar Ganduje. Hakan zai iya murkushe karfin Kwankwasiyya a jihar Kano.
4. Simon Bako Lalong
Gwamnan Filato, Simon Bako Lalong zai iya dacewa da wannan kujera. Sai dai ya goyi bayan Rotimi Amaechi ne a zaben APC, amma zai jawo kuri’un kiristoci.
5. Boss Mustapha
Wani Kiristan da zai iya kwadaito kuri’un wadanda ba Musulmai ba shi ne Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, ya fito ne daga Arewa maso yamma.
6. Kashim Ibrahim-Imam
Rahoton na Arise TV ya hada da Kashim Ibrahim-Imam wanda ya yi wa PDP takarar gwamna a Borno. Imam yana cikin mafi kusanci da ‘dan takaran na APC.
7. Abubakar Badaru
Shi ma Gwamnan Jigawa, Muhammadu Badaru Abubakar yana da karfi a jam’iyyar APC, har ya yi yunkurin ya nemi takara, daga baya sai ya janyewa Bola Tinubu.
8. Babagana Zulum
Farfesa Babagana Umara Zulum shi ne na karshe a jerin na mu. Gwamnan na Borno yana da farin jini a Najeriya, amma ya nuna bai sha’awar shiga siyasar kasa.
Rahoton da ya zo maku dazu ya nuna Asiwaju Bola Tinubu zai yi zama da Gwamnonin APC nan ba da dadewa ba domin tsaida abokin takararsa a zabe mai zuwa.
Babu mamaki kungiyar PGF ta gwamnonin APC ta taka rawar gani wajen dauko wani daga Arewa maso yamma ko maso gabas a tikitin jam'iyyar mai mulki.
Asali: Legit.ng