Tinubu da Atiku: Wurare 10 da aka samu kamanceceniya tsakanin manyan ‘yan takaran 2023
- Zaben 2023 zai kasance gumurzu musamman tsakanin Asiwaju Bola Tinubu da Atiku Abubakar
- Wadannan ‘yan siyasa sun yi tarayya wajen abubuwa da dama a rayuwarsu da tafiyar siyasarsu
- Har akwai masu ganin babu bambancin tasirin da za a gani duk wanda ya yi nasara a cikinsu a zaben
Legit.ng Hausa ta yi kokari tattaro alaka, kamanceceniya da tarayyar da ‘Dan takaran APC, Bola Tinubu ya yi da Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP.
1. Shekaru
A shekarar nan Atiku Abubakar zai cika shekara 76 a Duniya domin a haife shi ne a 1946. Shi kuwa Bola Tinubu a bana ya cika shekara 70 da haihuwa.
Kusan dukkaninsu sa’annin juna ne, tazarar shekara biyar ne tsakanin ‘yan takaran na 2023.
2. Dukiya
A wani rubutu da Mahmud Jega ya yi a shafinsa na Facebook, ya bayyana cewa dukkanin ‘yan siyasan biyu su na da arziki, attajirai ne na buga misali.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tun kafin shigarsa siyasa, Atiku Abubakar ya kai babban matsayi a aikin kwastam. Shi ma Bola Tinubu ‘dan kasuwa ne ko kafin ya zama gwamnan Legas.
3. Fara siyasa
Inda wadannan mutane suka kara yin tarayya shi ne sun shiga siyasa ne kusan a lokaci daya. A 1992 aka fara jin sunan Atiku da Tinubu da kyau a Najeriya.
Bola Tinubu ya zama Sanata a lokacin, shi kuwa Atiku ya yi takarar shugaban kasa. Tinubu yana tare da su MKO Abiola, Atiku yaronsu Shehu Yaradua ne.
4. Samun kujerar gwamnati
Bayan an dawo farar hula a 1999, Wazirin Adamawa da Jagaban suka lashe zaben gwamna a jihohinsu na Adamawa da Legas a karkashin AD da PDP.
Bola Tinubu ya yi shekaru takwas yana gwamna, shi kuwa Atiku ya samu damar tafiya Aso Villa.
5. Rasa madafan iko
Daga watan Mayun 2007 zuwa yanzu, mutanen nan biyu ba su rike wani mukami a gwamnati ba. Shekaru 15 kenan da Atiku Abubakar ya fita daga Aso Villa.
Shi ma Bola Tinubu ya bar kujerar gwamnan Legas a 2007, rana daya da abokin takaransa na yau.
6. Cin burin mulki
Inda wadannan ‘yan takara suka sake yin kama da juna a siyasa shi ne dukkaninsu sun dade su na neman yadda za su samu damar shugabantar Najeriya.
Atiku ya yi takara a 1992, 2007, 2011, 2015, da 2019, yayin da shi kuma Tinubu yake ta jiran 2023.
7. Zargin rashin gaskiya
Ana yi wa ‘yan siyasan biyu kallon marasa gaskiya wadanda suka amfana da baitul mali ko su na kan yi a dalilin kusancin da suka samu da kujerun gwamnati.
8. Akidar siyasa
Masu nazarin siyasa a Najeriya su na cewa jirgi daya ya dauko ‘dan takaran na jam’iyyar PDP da abokinsa na APC domin duk sun yi imani da tsarin jari hujja.
9. Rashin kaushi da ra’ayin rikau
A rubutunsa, 'dan jaridar ya tabbatar da Atiku da Tinubu a matsayin wadanda ba su da ra’ayin rikau a kan abin da ya shafi lamarin addini da kabilanci ko yanki.
Bola Tinubu ya na auren Kirista, Atiku kuwa ya auri Bayarabiya da Inyamura a cikin matansa.
10. Tarayya a jam’iyya
Kafin su raba jiha a siyasa, Wazirin Adamawa da Asiwaju Tinubu sun zauna tare a karkashin jam’iyyun SDP a 1992, ACN a 2007 da jam'iyyar APC a 2015.
Bayan Atiku ya yi takara ne ya bar ACN a 2007, sannan ya sauya-sheka daga APC a 2018.
Zabin 'dan takaran mataimaki
Dazu kun ji labari Bola Tinubu zai zauna da Gwamnonin APC a kan zabin Mataimakin Shugaban kasa bayan ya lashe tikitin zama ‘dan takara.
An ji cewa Bola Tinubu ya yi alkawari da Gwamnoni kuma da alama Gwamnonin Jihohin APC ne za su fito masa da abokin takara a Jam’iyya
Asali: Legit.ng