Zaben fidda gwanin APC: An fara kirgen kuri'u, Tinubu na gaba-gaba cikin 'yan takara

Zaben fidda gwanin APC: An fara kirgen kuri'u, Tinubu na gaba-gaba cikin 'yan takara

  • A yanzu haka an fara kirgen kuri'u a zaben fidda dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC da ke gudana a Eagles Square
  • Zuwa yanzu dai, babban jagoran jam'iyyar na kasa, Bola Ahmed Tinubu ne kan gaba a cikin masu neman tikitin jam'iyyar
  • Tun farko dai Tinubu ya samu akalla yan takara shida da suka hakura suka janye masa kafin deliget su fara kada kuri'a

Abuja - Tsohon gwamnan jihar Lagas, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, shine kan gaba a tseren takarar tikitin shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) yayin da aka fara kirgen sakamako a safiyar yau Laraba, 8 ga watan Yuni.

Ana ta yawan ambatan sunan Tinubu yayin da wadanda suka shirya zaben fidda dan takarar shugaban kasar jam’iyyar a Eagle Square ke tantance akwatunan zabe biyu, Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

Zaben fidda gwanin APC: Jerin 'yan takara 14 da suka ki janyewa, ake fafatawa dasu

Zaben fidda gwanin APC: Tinubu na gaba-gaba yayin da aka fara kirgen kuri'u
Zaben fidda gwanin APC: Tinubu na gaba-gaba yayin da aka fara kirgen kuri'u Hoto: Asiwaju Bola Tinubu
Asali: Twitter

Tinubu, wanda kafin a fara kada kuri’a ya samu goyon bayan yan takara shida, wadanda suka janye masa,yana gwabzawa da tsohon ministan sufuri, Mista Chibuike Rotimi Amaechi; da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo.

Yan takarar da suka janyewa Tinubu sune Gwamna Kayode Fayemi na jihar Ekiti; Sanata Godswill Akpabio; Farfesa Ajayi Borroffice; Mista Dimeji Bankole; Sanata Ibikunle Amosun; da Misi Uju Ohanenye.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Zaben fidda gwanin APC: Taro ya yi dumi, Osinbajo ya fice daga Eagle Square

A gefe guda, da sanyin safiyar Laraba ne Farfesa Yemi Osinbajo ya bar dandalin Eagles Square inda ake gudanar da zaben fidda gwani na shugaban kasa na APC, yayin da lamura ke kara fitowa fili cewa burinsa na ya gaji ubangidansa a matsayin shugaban kasar Najeriya mai yiwuwa ya ci tura.

Kara karanta wannan

Zaben fidda gwanin APC: Deliget din Jigawa ya yanki jiki, ya fadi matacce

Ana kyautata zaton Osinbajo ne kusa da tsohon gwamnan Legas Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a cikin ‘yan takara 23 da ke neman tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC a 2023, PM News ta ruwaito.

Sai dai abubuwan da suka faru a dandalin na Eagles Square sun nuna cewa mai yiwuwa ba zai samu damar nasara kan mutumin da ya fara nuna masa siyasa ba ta hanyar nada shi a matsayin babban lauya kuma kwamishinan shari’a a Legas.

Asali: Legit.ng

Online view pixel