Peter Obi da Atiku ba su yi barci da wuri ba, sun yi magana a kan zaben ‘dan takaran APC

Peter Obi da Atiku ba su yi barci da wuri ba, sun yi magana a kan zaben ‘dan takaran APC

  • Alhaji Atiku Abubakar ya tofa albarkacin bakinsa a kan zaben ‘dan takaran da jam’iyyar APC ta ke yi
  • ‘Dan takaran na PDP ya ce gwamnati mai-ci ba ta iya cika alkawuran da ta yi wa mutanen Najeriya ba
  • Shi ma Peter Obi ya yi kira ga matasa yayin da APC ta ke fito da wanda zai yi mata takara a zaben 2023

Abuja - A yau Laraba ne ake sa ran sanin wanda zai yi wa jam’iyyar APC mai mulki takarar kujerar shugaban Najeriya a zaben shekara mai zuwa na 2023.

Legit.ng Hausa ta kawo maku rahoto cewa tun jiya da rana aka soma tantance takara, zuwa yamma kuma aka fara kiran masu takara su gabatar da jawabi.

Sai bayan dare ya tsala sannan aka fara kada kuri’u a zaben fitar da gwanin na jam’iyyar APC.

Kara karanta wannan

Tsohon Ministan Buhari ya buge da cacar-baki a filin zaben ‘dan takarar shugaban kasa

Yayin da masu neman takara suke jawabi a wajen zaben, ‘dan takarar jam’iyyar hamayya ta PDP, Atiku Abubakar ya fito ya na magana a shafinsa na Twitter.

Wazirin na kasar Adamawa ya nuna cewa jam’iyyar APC mai mulki ba za ta iya cewa ta cika alkawuran da ta yi wa mutanen kasa har suka zabe ta a 2015 ba.

Abin da Atiku Abubakar ya fada

“Jam’iyyar APC za ta iya neman boye komai amma ban da batun cika alkawuran da ta yi wa ‘Yan Najeriya su ka zabe ta.”

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“Zaben 2023 dama ce da mutanen kasa za su yi zabe kan manufofin da gwamnatin nan ta gaza.”

- Atiku Abubakar

Peter Obi da Atiku
Atiku Abubakar da Peter Obi a zaben 2019 Hoto: www.thecable.ng
Asali: UGC

Atiku Abubakar wanda zai yi takarar shugaban kasa a PDP a 2023 ya yi wannan magana ne da karfe 11:18 na dare, don haka wasu ke cewa bai iya yin barci ba.

Kara karanta wannan

Shugaban APC na kasa ya bada sharadin cancanta da zama Magajin Buhari a zaben 2023

Rahoton Legit.ng ya nuna Peter Obi bai yi barci da wuri ba, domin ya yi magana a Twitter kusan karfe 10:30, yana tofa albarkacin bakinsa a kan zaben na APC.

Peter Obi ya yi kira ga matasa

“Ya ku matasan Najeriya, yayin da ku ke sauraron masu neman takara a jam’iyya mai mulki su na yakin neman tikiti…
…ku yi tunani, kuma ku tambaya ko a gobe za su iya ba ku abin da ba ba su bada a cikin tsawon shekaru bakwai ba;
...Ko kuma kun fi ji dadi a yau fiye a shekaru bakwai da suka wuce.” - Peter Obi.

Rade-radi a kan takarar Tinubu

Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya fitar da sanarwa yana cewa sai bayan an tabbatar da nasararsa a zaben tsaida gwani, sannan zai yi maganar wanene mataimakinsa.

A halin yanzu ana fadawa mutane cewa Bola Tinubu zai dauki Musulmi ne ya zama masa mataimaki, ba za a tafi da kirista a tikitin APC ba a zabe mai zuwa ba.

Kara karanta wannan

Zaben fidda gwanin APC: Zan amshi sakamakon da zuciya daya – Yerima

https://hausa.legit.ng/siyasa/1473502-tinubu-ya-karyata-labarin-sharrin-da-ake-yi-masa-ana-tsakiyar-zaben-dan-takara-a-apc/

Asali: Legit.ng

Online view pixel