Za ku taro rikici: Yahaya Bello ya fadi abu daya da zai hana shi takara a zaben fidda gwanin APC
- Dan takarar shugaban kasa a APC ya fusata, ya bayyana abu daya da zai sa ya janye daga takarar shugaban kasa
- Ya kuma bayyana cewa, wasu shugabannin APC da gwamnonin Arewa na shirya masa makarkashiya
- Ya bayyana haka ne yayin da gwamnonin ke kokarin zabge da yawa daga cikin 'yan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC
Abuja - Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi ya gargadi jam'iyyar APC, cewa cire sunansa a jerin 'yan takarar shugaban kasa da za su gwabza a zaben fidda gwani na yau daidai yake da kunno wutar rikici, Vanguard ta ruwaito.
Gwamna Bello, wanda yana daya daga cikin ’yan takara 23 a jam’iyyar, ya ce akwai makarkashiyar da ake shirya masa, inda ya zargi gwamnonin APC na Arewa da wasu jigai-jigai da kitsa manakisa akansa.
Shugaba Buhari ne kadai zai sa na janye - Yahaya Bello
Bello wanda ya bayyana kansa a matsayin dan takara mafi karbuwa da zai yi nasara idan har tsarin ya tafi daidai, ya ce abu daya ne zai hana shi ya tsayawa takarar shugaban kasa shi ne idan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce ya janye daga takarar, inji The Nation.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Da yake zantawa da manema labarai a fadar gwamnati bayan ganawar sirri da shugaban kasa, Bello ya ce jam’iyyar APC za ta ci gaba da rike madafun iko idan har ta yi bi ka’ida.
A kalamansa:
"Shigowa cikin fage a yau, zan yi nasara sosai idan tsarin ya tafi daidai."
Ya ce babu bukatar a cire shi a zaben fidda gwanin, yana mai bayyana cewa, yana wakiltar matasa da wadanda aka zalunta ne.
Bello ya ce gwamnonin APC na Arewa ba su tuntube shi ba a lokacin da suka dauki kudurin cewa mulki ya koma Kudu, kuma kudurin bai masa ba.
Ya kuma kara jaddada adawarsa ga tsarin shugabancin karba-karba, yana mai cewa hakan ba zai bayar da damar samun wanda ya cancanta ya tafiyar da al’amuran kasar nan ba.
El-Rufai: Dalilin da yasa Yahaya Bello ya fice a taron Buhari da gwamnonin APC na Arewa
A wani labarin, gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, ya ce Yahaya Bello, gwamnan Kogi, ya fita daga taron gwamnonin jam’iyyar APC na Arewa da shugaban kasa Muhammadu Buhari saboda uzuri.
El-Rufai ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da manema labarai a ranar Litinin bayan gwamnonin sun kammala ganawarsu da Buhari, TheCable ta ruwaito.
Da yake jawabi ga manema labarai, El-Rufai ya ce gwamnoni 13 daga cikin 19 na APC daga Arewa sun amince da cewa a mika tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar zuwa Kudu.
Asali: Legit.ng