Obasanjo da Babangida ba su nufin kasar nan da alheri – Mansur Malumfashi

Obasanjo da Babangida ba su nufin kasar nan da alheri – Mansur Malumfashi

- Wani Farfesan Jami’a yace su IBB da Obasanjo su ka kashe Najeriya

- Mansur Malumfashi yace ana kokarin kawowa Shugaba Buhari cikas

- Tsofaffin Shugaban kasar sun nemi Buhari ya hakura da sake takara

Wani babban Farfesa a Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa ta Jihar Bauchi watau Farfesa Mansur Malumfashi ya soki tsofaffin Shugabannin kasar nan Cif Oluesgun Obasanjo da Ibrahim.

Obasanjo da Babangida ba su nufin kasar nan da alheri – Mansur Malumfashi
IBB da Obasanjo sun nemi Buhari ya hakura da zaben 2019

Farfesa Mansur Malumfashi yace su Obasanjo da Babangida ba su nufin Najeriya da alheri. Farfesan ya bayyana wannan ne a inda ya gabatar da wata takarda a wajen wani taron Kungiyar ‘yan kwadago na kasar nan da aka yi a Jihar Bauchi.

KU KARANTA: Yadda aka sace 'Yan mata a Garin Dapchia a Jihar Yobe

Malumfashi yace idan akwai irin su Janar Obasanjo da kuma IBB, kasar nan ba za ta je ko ina ba. Farfesa Malumfashi yace makiya ne ke kokarin yi wa Shugaba Buhari zaman kasa saboda yakin da yake yi da rashin gaskiya da yake yi a kasar.

Malamin Jami’ar ya bayyanawa Jama’a cewa Obasanjo da Babangida sun samu damar da za su gyara kasar nan amma ba su yi wani abin kirki. Tsofaffin Shugabannin dai sun soki Shugaba Buhari sun nemi ya hakura da mulki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng