Kowa ya bi: An sake samun Gwamnan Arewa da ke goyon bayan ‘Yan kudu su karbe mulki

Kowa ya bi: An sake samun Gwamnan Arewa da ke goyon bayan ‘Yan kudu su karbe mulki

  • Gwamna Abdulrahman AbdulRazaq ya ce shi ma yana goyon bayan shugabanci ya bar Arewa a 2023
  • Abdulrahman AbdulRazaq bai cikin wadanda suka sa hannu a takardar da Gwamnoni suka fitar da farko
  • Yanzu Yahaya Bello ne kadai bai tare da shugabannin Arewa na APC a kan mikawa Kudu mulki

Kwara - Gwamna Abdulrahman AbdulRazaq na jihar Kwara ya ce yana goyon bayan matsayar shugabannin Arewa na cewa a kai mulki kudu a 2023.

Mai girma Gwamna Abdulrahman AbdulRazaq ya bayyana haka ne a lokacin da yake maidawa jaridar Daily Trust ganin cewa ba a ga sa hannunsa ba.

Abdulrahman AbdulRazaq bai cikin gwamnonin APC na shiyyar Arewacin Najeriya da suka hadu a kan a fito da ‘dan takarar shugaban kasa daga kudu.

Kara karanta wannan

Babban abin da ya sa Gwamnonin Arewa ba su so Lawan ya zama Shugaban kasa inji Uzor Kalu

Gwamnan ya ce tun da takardar matsayar gwamnonin ta fito, aka tasa shi a gaba domin jin inda ya sa gaba a game da zaben magajin Muhammadu Buhari.

Uzurin da Gwamnan ya bada

Daily Trust ta rahoto AbdulRazaq yana cewa bai iya sa hannu a takardar ba ne domin bai samu halartar zaman da gwamnonin suka yi ba a ranar Asabar.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Bashir Adigun wanda shi ne ke taimakawa gwamnan Kwara wajen yada labaran siyasa, ya fitar da jawabi na musamman yana mai bayanin abin da ya faru.

Gwamnonin Arewa
Gwamnonin Arewa na APC Hoto: @govkaduna
Asali: Facebook

Gwamna AbdulRazaq ya ce bada auren wata diya a wurinsa ya hana shi zuwa wajen taron.

A karshe sauran gwamnonin ba su iya jiran AbdulRazaq ya sa hannu ba domin ana kokarin ayi maza a aikawa shugaba Muhammadu Buhari takardar.

Daga karshe ya sa hannu

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Buhari ya magantu kan hanyar da za a bi wajen zabar dan takarar APC

Amma a karshe an kawowa Gwamnan na jihar Kwara takardar matsayar gwamnonin, kuma ya rattaba hannunsa a kai domin nuna su na kan shafi daya.

Kamar yadda Bashir Adigun ya bayyana a jawabin na sa, Mai gidansa ne ya zama mutum na 12 da ya sa hannu, yana goyon shugabanci ya koma kudu a 2023.

Hakan yana nufin kan duka gwamnonin Arewa ya hadu a kan wannan matsaya face Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello wanda yake neman shugabanci.

Mu na kan maganarmu

A ranar Litinin aka ji labari Gwamnonin Arewacin Najeriya su na nan a kan matsayarsu na cewa sai an ba kudu takara a 2023, ba su tare da Ahmad Lawan.

Gwamna Simon Bako Lalong ya fadawa Duniya cewa abokan aikinsa sun yi zama da Muhammadu Buhari a Aso Villa, kuma sun nanata masa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel