Da dumi-dumi: Shugaban APC ya fusata, ya fatattaki 'yan jarida a sakateriyar APC

Da dumi-dumi: Shugaban APC ya fusata, ya fatattaki 'yan jarida a sakateriyar APC

  • Yanzu wasu rahotanni daga Abuja ke cewa, shugaban APC ya fusata, ya sa a fatattaki 'yan jarida daga bakin sakateriyar APC
  • Wannan na zuwa ne daidai lokacin da ake kai ruwa rana a jam'iyyar kan batun dan takarar shugaban kasa
  • Ya zuwa yanzu dai ba a san me jam'iyyar ta yanke kan batu zabo magajin shugaba Buhari a zaben 2023 ba

Abuja - Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya fatattaki ‘yan jarida da aka amince da su da ke daukar labaran jam’iyyar daga sakatariyar ta na kasa da ke Abuja rahoton Leadership.

Daya daga cikin jami’an tsaro a sakatariyar, wanda ya mika bayanan ga manema labarai tare da neman su fice daga harabar sakatariyar jam’iyyar, ya ce suna aiki ne da umarnin shugaban jam’iyyar na kasa.

Ya ce Adamu ya ce su fitar da ‘yan jarida daga sakatariyar a kan cewa zai dawo sakatariyar ne domin yin taro, kuma wurin ya cika makil.

Da dumi-dumi: Shugaban APC ya fusata, ya fatattaki 'yan jarida a sakateriyar APC a yau dinnan
Da dumi-dumi: Shugaban APC ya fusata, ya fatattaki 'yan jarida a sakateriyar APC | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Wannan na zuwa ne sa’o’i kadan bayan kwamitin ayyuka na jam’iyyar (NWC) ya nesanta kansa da batun Adamu kan amincewa da shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An ce Adamu ya bayyana Lawan a matsayin dan takarar maslaha a taron NWC a Abuja ranar Litinin.

Ya shaida wa ’yan NWC cewa ya yanke zabin Lawan ne bayan ya tattauna da shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Har yanzu daia ana ci gaba da cece-kuce kan yadda jam'iyyar ke shirinta na tsayar da dan takara.

Daga karshe: Dan takarar shugaban kasa a APC ya janye saboda wasu dalilai

A wani labarin, Ken Nnamani, tsohon shugaban majalisar dattawa, ya fice daga takarar neman tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, TheCable ta ruwaito.

Tsohon dan majalisar ya bayyana janyewarsa ne a wata ganawa da ya yi da manema labarai a Abuja ranar Litinin.

Ya bayyana cewa:

“A halin da ake ciki yanzu, ba wani ma’ana in ci gaba da takara domin ban samu damar tallata bayanai na da ra’ayoyina ga wakilan jam’iyyarmu ba ta hanyar da za ta ba da damar shawarwari da fahimtar juna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel