Dan takarar shugaban kasa a APC: Bidiyon yadda Yahaya Bello ya bar taron gwamnonin APC a fusace

Dan takarar shugaban kasa a APC: Bidiyon yadda Yahaya Bello ya bar taron gwamnonin APC a fusace

  • Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya bar wani taron ganawa da takwarorinsa a fusace kan batun mika mulki yankin kudu
  • Bello dai na daya daga cikin manyan yan takara da ke neman tikitin takarar shugaban kasa na APC daga yankin arewacin kasar
  • A lokuta da dama gwamnan ya jadadda cewa ba zai janyewa kowa ba gabannin zaben fidda gwanin jam’iyyar mai mulki

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

A ranar Litinin, 6 ga watan Yuni, Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi, ya yi watsi da shawarar takwarorinsa na mika tikitin shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) zuwa kudu.

A cikin wani bidiyo da ya shahara, an gano yadda Bello ya fito daga wani taro a fusace, yayin da Gwamna Abdullahi Sule na Nasarawa ke kokarin lallashinsa.

Dan takarar shugaban kasa a APC: Bidiyon yadda Yahaya Bello ya bar taron gwamnonin APC a fusace
Dan takarar shugaban kasa a APC: Bidiyon yadda Yahaya Bello ya bar taron gwamnonin APC a fusace Hoto: @OfficialGYBKogi
Asali: Twitter

Hakazalika an jiyo Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno da ya fito a bayansu yana bashi hakuri.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Buhari ya magantu kan dan takarar da yake so ya gaje shi

Bidiyon ya bayyana ne jim kadan bayan gwamnonin APC na arewa sun gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari kan hukuncinsu na son APC ta mika tikitinta na shugaban kasa yankin kudu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da yake magana kan dalilin da yasa Bello bai kasance a taron ba, gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya ce mai neman takarar shugaban kasar yana adawa da hukuncin gwamnonin na mika mulki kudu, jaridar The Cable ta rahoto.

Sai dai kuma, shugaban jam’iyyar na kasa, Abdullahi Adamu ya sanar da shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan a matsayin dan takarar maslaha na jam’iyyar.

Amma mambobin kwamitin aiki na APC sun yi adawa da matsayin Adamu.

Zaben fidda gwanin APC: Jerin jihohin da Tinubu, Osinbajo da sauran yan takara za su iya lashewa

A gefe guda, wani rahoton nazari daga jaridar The Nation ya yi hasashen Asiwaju Bola Ahmed Tinubu zai lashe zaben fidda dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da aka shirya yi a ranar Talata, 7 ga watan Yuni, a Abuja.

Kara karanta wannan

Taron APC: Har yanzu Buhari bai zartar da hukunci kan mika mulki kudu ba - Badaru

A cewar rahoton, Tinubu, tsohon gwamnan jihar Lagas, yana da kwarjini, isa, tsari, goyon baya, farin jini, tarihin nasara, da kwarewar aiki sosai a bangarorin gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu.

Tinubu wanda ya kafa APC tare da shugaba Buhari da sauran masu ruwa da tsaki ya kuma horar da yan siyasa a fadin kasar nan, wanda da dama daga cikinsu suka zama gwamnoni, sanatoci, yan majalisar wakilai da sauransu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel