Yadda Bola Tinubu ya sha gaban Osinbajo, Amaechi, Lawan da duk masu neman takara

Yadda Bola Tinubu ya sha gaban Osinbajo, Amaechi, Lawan da duk masu neman takara

  • Hasashe da nazarin da Daily Trust ta yi bayan la’akari da yadda abubuwa ke tafiya a APC ya nuna Bola Ahmed Tinubu ya yi gaba a wajen samun takara
  • Gwamnonin APC ke da wuka da nama a jihohin da suke mulki, a jihohin adawa kuwa, sai abin da tsofaffin gwamnoni, ministoci da sauran kusoshi suka yi
  • A masu neman tikiti a APC, babu wanda ya gana da masu zaben ‘dan takara kamar Yemi Osinbajo, Ahmad Lawan, da shi karon kansa, Bola Tinubu

Jaridar ta ce abin ba a haduwa da masu kada kuri’a a zaben fitar da gwani ba ne, ana bukatar sanayya da alaka da masu juya akalar jam’iyya a jihohi.

A wannan bangare ana tunanin Bola Tinubu yana da jihohi akalla 16 da zai samu kuri’u sosai.

Kara karanta wannan

Gwamnonin APC sun tattauna da NWC, Adamu bai samu halarta ba

Hasashen ya na nuna sauran ‘yan takaran ba za su iya mamaye fiye da jihohi biyu ba. A jihohi 11, ana tunanin kowane mai takaran a APC zai yagi rabonsa ne.

Farfesa Yemi Osinbajo zai iya karbe duka kuri’un ‘ya ‘yan APC a zaben fitar da gwani daga Ogun da Nasarawa. Ahmad Lawan yana tare da jihohin Yobe da Imo.

Dr. Kayode Fayemi zai samu Ekiti da Anambra, sai Rotimi Amaechi yana da Ribas da Filato.

Su kuwa Yahaya Bello, Ben Ayade, Godswill Akpabio, Ogbonnaya Onu za su yi nasara ne a jihohinsu, watakila bayan nan babu wata jiha da za su yi galaba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bola Tinubu
Bola Ahmed Tinubu Hoto: @officialasiwajubat
Asali: Facebook

Inda Tinubu zai mamaye

Daga cikin jihohin da Daily Trust ta ke ganin Bola Tinubu zai samu kuri’u sosai akwai; Kano, Kaduna, Katsina, Borno, Sokoto, Legas, Osun, Neja, da Adamawa.

Kara karanta wannan

Maslaha: An bayyana shugaban majalisa Lawan a matsayin dan takarar APC

Sauran jihohin da Tinubu ya karbe su ne: Bauchi, Ondo, Kwara, Benue, Edo, Delta da kuma Zamfara. Sai dai idan labari ya canza kafin lokacin zaben gwani.

Manya da Gwamnonin da ke tare da Tinubu

Bisa dukkan alamu, Gwamnoni irinsu Abdullahi Ganduje, Aminu Bello Masari, Nasiru El-Rufai, Abubakar Sani Bello duk su na goyon bayan takarar Tinubu ne.

Har ila yau jigon na APC yana da goyon bayan Babagana Zulum da Mai gidansa, Kashim Shettima.

Legit.ng Sauran jiga-jigan APC da suke wannan sahu sun hada da; Sanata Aliyu Wamakko, George Akume, Adamu Adamu da irinsu Sanata Abu Ibrahim.

Yahaya Bello su janye takara

Kun ji labari cewa kwamitin yakin neman zaben Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya yabawa Gwamnonin APC na Arewa kan sallamawa Kudu takara a zaben 2023.

Masu taya Bola Tinubu kamfe suka ce akwai bukatar duk wani ‘Dan Arewa ya janye. Gwamna Yahaya Bello da Ahmad Sani Yariman Bakura sun ki janye takararsu.

Kara karanta wannan

Tashin nakiya a coci: Ana ta zaben fidda gwani, Tinubu ya tafi jihar Ondo ziyara

Asali: Legit.ng

Online view pixel