Mutanen Bola Tinubu sun bukaci wasu ‘yan siyasa 3 su gaggauta janye takarar Shugaban kasa

Mutanen Bola Tinubu sun bukaci wasu ‘yan siyasa 3 su gaggauta janye takarar Shugaban kasa

  • Kwamitin yakin neman zaben Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya yabawa Gwamnonin APC na Arewa
  • Gwamnonin jihohin Arewacin Najeriya sun yarda shugaban kasan 2023 ya fito daga yankin Kudu
  • Saboda haka masu taya Bola Tinubu kamfe suka ce akwai bukatar duk wani ‘Dan Arewa ya janye

Abuja - Kwamitin yakin neman zaben Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya nemi ‘yan siyasan Arewa da ke neman tikitin zama shugaban kasa a APC su hakura.

The Cable ta ce kwamitin yakin zaben ya na so Dr. Ahmad Lawan, Yahaya Bello da Sanata Ahmad Sani Yariman Bakura su bar maganar neman takaran 2023.

A ranar Lahadi, 5 ga watan Yuni 2022, masu taya Bola Tinubu yaki wajen ganin ya zama shugaban Najeriya, suka fitar da jawabi, su na wannan kira.

Kara karanta wannan

2023: Kowa ya cije kan bakansa, an gaza yin sulhu da Tinubu da su Osinbajo a takaran APC

Hakan yana zuwa ne bayan gwamnonin Arewa na APC sun amince cewa ya kamata a dauko ‘dan takarar shugaban kasa a zaben 2023 ne daga yankin Kudu.

Bayo Onanuga ya yi magana

Ganin matsayar da shugabannin na shiyyar Arewa suka dauka, Bayo Onanuga ya yabawa gwamnonin, na daukar hanyar zaman lafiya da cigaban kasa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Jaridar ta rahoto Bayo Onanuga wanda shi ne kakakin kwamitin yakin neman zaben yana cewa ya kamata duk masu kaunar Najeriya su yabawa gwamnonin.

Bola Tinubu
Bola Tinubu yana jawabi Hoto: punchng.com
Asali: UGC

A jawabin da Onanuga ya fitar, ya bayyana gwamnonin na Arewa a matsayin masu kishi.

Wannan matsaya da gwamnoni na APC suka hadu a kai, ya kawo karshen duk wani rashin tabbas da dar-dar da aka shiga a jam’iyya mai mulki a cewar shi.

Ya kamata ayi koyi da Badaru

Har ila yau, kakakin kwamitin neman zaben na Bola Tinubu, ya yabawa Gwamnan Jigawa, Abubakar Badaru wanda ya yi maza ya fasa shiga wannan takara.

Kara karanta wannan

Ba zai taba goyon bayan Tinubu ba: Sule Lamido ya bayyana mutum 2 da Buhari yake so ya tsayar a 2023

Wannan ya sa kwamitin suka bukaci sauran ‘yan takara irinsu Ahmad Lawan, Gwamna Yahaya Bello da tsohon Gwamna, Ahmed Rufai Sani Yerima su janye.

Kamar yadda Onanuga ya bayyana, idan wadannan ‘yan siyasa na Arewa suka bi sahun Gwamna Badaru, tarihin siyasa ba zai taba fasa ambatonsu da alheri ba.

Badaru ya bada wuri a APC

Rahoton da mu ka fitar a karshen makon jiya ya nuna cewa Gwamnan jihar Jigawa ya zama na farko da ya fita daga masu neman takarar shugaban kasa a APC.

Sauran Gwamnonin na APC suka bada sanarwar cewa Muhammad Badaru Abubakar ya janye burin da yake da shi na karbar shugabancin kasa a shekarar badi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel