Mutumin da ya fara kai Osinbajo wajen Bola Tinubu ya na nadama saboda takarar 2023

Mutumin da ya fara kai Osinbajo wajen Bola Tinubu ya na nadama saboda takarar 2023

  • Bayo Onanuga ya fito yana cewa shi ne silar haduwar Yemi Osinbajo da Asiwaju Bola Tinubu
  • Rikakken ‘dan jaridar ya ce a yau yana yin nadamar kai Farfesa Osinbajo wajen Tinubu a 1999
  • Tinubu ya shigo da Osinbajo cikin harkar siyasa, amma tsohon yaron na sa yana takara da shi

Abuja - Fitaccen ‘dan jarida kuma kakakin Bola Tinubu Campaign Organisation, Bayo Onanuga ya yi ikirarin kai Yemi Osinbajo gaban Asiwaju Bola Tinubu.

Punch ta rahoto Bayo Onanuga yana cewa shi ne wanda ya kai Farfesa Yemi Osinbajo wajen Asiwaju Bola Tinubu a lokacin yana gwamnan Legas a 1999.

Kamar yadda muka samu labari, Onanuga ya yi wannan bayani ne a jawabin da ya fitar a ranar Litinin a matsayin martani kan kalaman Buba Galadima.

Mai magana da yawun kwamitin yakin zaben jigon na APC ya ce a yau yana nadamar hada Tinubu da Osinbajo wanda ya zama mataimakin Buhari.

Kara karanta wannan

Maslaha: An bayyana shugaban majalisa Lawan a matsayin dan takarar APC

Osinbajo: Malamin Jami'a a 1999

A rubutun da ya yi, Mista Onanuga ya ce Osinbajo yana malamin jami’a a 1999 a lokacin da Tinubu yake kokarin nada wadanda zai ba mukamai a gwamnati.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

‘Dan jaridar yace Bola Tinubu ya yi niyyar nada Bayo Oriola a matsayin kwamishinan shari’ansa, amma daga baya sai aka bukaci shi ya kawo sunan wani.

Osinbajo
Farfesa Yemi Osinbajo a gaban kwamitin APC Hoto: @professoryemiosinbajo
Asali: Facebook

Nan take sai Onanuga yace ya bada sunan abokinsa Yemi Osinbajo, hakan ya sa aka cire Oriola.

Bayo Onanuga ya bada Oriola hakuri

“Yanzu ina da-na-sanin abin da nayi a Junairun 1999. Zan ce ina nadama, musamman tun da danyen aikin nawa bai yi wa Bayo Oriola dadi ba.
Ina mai sake bada hakuri ga Bayo Oriola. Ban taba tunanin abubuwa za su sake zani tsakanin Tinubu da Osinbajo, wanda na bada sunansa ba.”

Kara karanta wannan

Tashin nakiya a coci: Ana ta zaben fidda gwani, Tinubu ya tafi jihar Ondo ziyara

- Bayo Onanuga

An rahoto Onanuga yana cewa da Tinubu ya ji yana yabon Osinbajo, sai ya bukaci ya zauna da shi. Onanuga ne ‘dan sakon da ya je gida domin ya gayyato shi.

Tsohon shugaban na NAN yake cewa bai taba ba kowa wannan labari ba, amma ya nemi afuwar kafar da ya yi Oriola duk da yadda ya yi wa Tinubu kamfe.

PDP za ta sake yin zabe a Legas

Dazu kun samu labari cewa biyo bayan rikicin da ake ta yi a jam’iyyar PDP ta jihar Legas, shugabanni sun bar 'Yan PDP a duhu a kan shirye-shiryen 2023.

Har yau PDP ba ta san ‘yan takarar majalisar ta a Legas ba, murna ta leko ta komawa ‘ya ‘yan jam’iyyar adawan da suka samu takara, za a sake yin zabe a yau.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng