‘Yan takara na cikin rashin tabbas, PDP za tayi sabon zaben fitar da gwanin ‘Yan Majalisa
- Akwai shirin gudanar da wani sabon zaben fitar da gwani da jam’iyyar PDP ta ke yi a jihar Legas
- A yau ake tunanin uwar jam’iyya za ta zabi wadanda za su yi wa PDP takarar ‘yan majalisa a jihar
- Hakan ya biyo bayan ruguza zaben ‘yan takarar majalisar tarayya da shugabannin PDP suka yi
Lagos - ‘Yan takara sun samu kansu a wani irin yanayi a jam’iyyar PDP na reshen jihar Legas a dalilin shirin sake gudanar da zabukan fitar da gwani.
Daily Trust ta rahoto cewa a ranar Litinin, 6 ga watan Yuni, 2022 jam’iyyar hamayyar za tayi sababbin zabukan fitar da gwani na kujerun ‘yan majalisa.
A yau ‘yan takarar kujerun majalisar wakilan tarayya da ake da su a Legas za su san makomarsu.
Wani jigo na jam’iyyar PDP a jihar Legas ya shaidawa jaridar cewa ana ta yin nuku-nuku game da shirin sabon zaben tun bayan soke na farko da aka yi.
Shugabannin gudanarwa na PDP na reshen Legas, sun yi watsi da zabukan da aka gudanar a ranar 22 na Mayu bisa zargin taba sunayen masu zabe.
SWC ta na zargin an yi wasa da sunayen wadanda suke tsaida ‘dan takara, don haka aka sa rana domin a gudanar da wani sabon zaben na fitar da gwani.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An bar 'Yan PDP a duhu
Har zuwa ranar Lahadin nan da ta wuce, da yawa daga cikin ‘ya ‘yan jam’iyyar PDP ba su san halin da ake ciki a game da shirin sabon zaben da za ayi ba.
Wani daga cikin shugabannin gudanarwa ya ce yana cikin ‘yan kwamitin SWC na jihar Legas, amma shi kan shi bai san yaushe za a gudanar da zaben ba.
Aiki ya koma kan NWC
Da aka tuntubi Sakataren yada labarai na PDP na jihar, Hon. Akeem Amode, ya tabbatar da cewa zabukan za su kankama ne a yankunan majalisun tarayya.
An rahoto Akeem Amode yana cewa za ayi zaben ne a kowace mazaba 24 domin fitar da ‘yan takaran da za su tsayawa jam'iyyar a babban zabe mai zuwa.
Da aka nemi jin ko uwar jam’iyya ta san da wannan magana, Hon. Amode ya tabbatar da cewa ‘yan kwamitin NWC na kasa ne za su gudanar da zabukan.
Banky W ya samu takara
Kwanaki kun ji labari cewa jam’iyyar PDP za ta tsaida Olubankole Wellington (Banky W) a matsayin ‘dan takaran yankin Eti-Osa bayan ya lashe zabe.
A lokacin an ji Olubankole Wellington zai gwabza da wanda APC ta ba tikiti a takarar ‘dan majalisa, to sai da yanzu wannan takarar ta na lilo ne a iska.
Asali: Legit.ng