2023: Osinbajo, Tinubu Da Masu Neman Takara Daga Kudu Maso Yamma Za Su Yi Taro Gabanin Zaben Fidda Gwanin APC
- Ana kyautata zaton masu neman takarar shugaban kasa karkashin inuwar jam'iyyar APC za su yi wani taro a daren yau a Jihar Ogun
- Hakan na zuwa ne yayin da jam'iyyar mai mulki a kasa ke tunkarar babban taronta inda za a zabi dan takarar shugaban kasa na zaben 2023
- Wadanda aka fatan za su hallarci taron sun hada da dukkan yan takarar daga kudu, gwamnonin yankin kudu maso yamma da masu ruwa da tsaki
Ana fatan masu neman takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar APC za su yi taro a yau Asabar.
A cewar The Punch, za a yi taron ne misalin karfe 8 na dare a gidan Otunba Osoba, tsohon gwamnan Jihar Ogun.
Wannan cigaban na zuwa ne bayan jam'iyyar na APC ta kammala tantance masu neman takarar shugaban kasar.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A ranar Juma'a, John Oyegun, shugaban kwamitin tantance yan takarar ya sanar da cewa an soke takarar mutum 10 cikin masu neman takarar 23 da ake fatan za su fafata a zaben fidda gwanin.
Amma, Oyegun bai ambaci sunan wadanda aka tantance din ba kawo yanzu.
Masu neman takarar shugaban kasar daga kudu maso yamma sun hada da Bola Ahmed Tinubu, tsohon gwamnan Legas, Mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, Kayode Fayemi, gwamnan Jihar Ekiti da Ibikunle Amosun, tsohon gwamnan Ogun.
Saura sun hada da Dimeji Bankole, tsohon kakakin majalisar wakilai na tarayya, Rob Borrofice, sanata mai wakiltar Ondo North da Tunde Bakare, shugaban cocin Citadel Global Community.
Ana fatan gwamnonin jihohin kudu maso yamma za su hallarci taron.
The Cable ta tuntubi Yinka Oyebode, kakakin Fayemi don tabbatar da labarin amma ya ce ba zai iya tabbatarwa ba.
"Ba zan iya tabbatarwa ba. Zan tuntube ka idan an yi taron," in ji shi.
Jubril Gawat, babban hadimin Babajide Sanwo-Olu, gwamnan Jihar Legas shima ya ce "ba shi da masaniya kan taron".
Za a yi zaben fidda gwanin na APC ne daga ranar 6 zuwa 8 na watan Yuni.
Ba Zan Taɓa Raina Buhari Ba, In Ji Bola Tinubu
A wani rahoton, Bola Tinubu, tsohon gwamnan Jihar Legas kuma mai neman takarar shugabancin kasa a APC, ya ce ba zai dace ya ci mutuncin Shugaba Muhammadu Buhari ba, The Cable ta rahoto.
Tinubu ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da kungiyar yakin neman zabensa ta fitar game da jawabinsa yayin ganawa da deliget a Jihar Ogun.
A wurin taron, mai neman takarar shugaban kasar ya ce ba domin shi ba da Buhari ya sha kaye a zaben shugaban kasa na shekarar 2015.
Asali: Legit.ng