Wike Ya Ziyarci Atiku a Yayin Da PDP Ke Neman Mataimakin Shugaban Kasa Daga Kudu

Wike Ya Ziyarci Atiku a Yayin Da PDP Ke Neman Mataimakin Shugaban Kasa Daga Kudu

  • Nyesom Wike, gwamnan Jihar Rivers ya ziyarci dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar a ranar Laraba
  • Wannan ziyarar na zuwa ne bayan shi Atikun ya fara kai wa Gwamna Wike ziyara bayan kammala zaben fidda gwani na jam'iyyar PDP
  • Duk da cewa kawo yanzu ba a bayyana abin da suka tattauna ba, ana hasashen ziyarar ba za ta rasa nasaba da zaben wanda zai yi wa Atiku mataimaki ba daga Kudu

FCT, Abuja - Gwamnan Jihar Rivers, Nyesom Wike, a rana Laraba da yamma ya ziyarci dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a babban zaben 2023, Atiku Abubakar a gidansa da ke Abuja, The Punch ta rahoto.

Ziyarar na Wike na zuwa ne a lokacin da Atiku da babban jam'iyyar hammayar ke neman mataimakin shugaban kasa da za a amince da shi daga yankin kudu.

Kara karanta wannan

Jerin sunayen 'yan takara 5 da ake sa ran Buhari zai zabi daya don ya gaje shi

Wike Ya Ziyarci Atiku a Yayin Da PDP Ke Neman Mataimakin Shugaban Kasa Daga Kudu
Wike Ya Ziyarci Atiku a Yayin Da PDP Ke Neman Mataimakin Shugaban Kasa Daga Kudu. Hoto: @atiku.
Asali: Twitter

Shugaban kwamitin amintattu, BOT, na PDP, Walid Jibrin, a ranar Litinin ya ce, "BOT za ta taimakawa jam'iyyar kuma tabbas Atikun zai fitar da mataimaki daga kudancin Najeriya wanda za a amince da shi."

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Atikun, wanda kuma shine dan takarar shugaban kasa na PDP a zaben 2019, ya yi takara tare da tsohon gwamnan Jihar Anambra, Peter Obi wanda ya bar PDP ya koma Labour Party inda zai yi takarar shugaban kasa a 2023.

The Punch ta gano cewa Wike ya mayar da karamcin ziyarar da tsohon mataimakin shugaban kasar Atiku ya kai masa ne a ranar Litinin.

An hangi fuskar Wike cike da annashuwa akasin ziyarar baya

Akasin ziyarar ranar Litinin inda aka ga fuskar Wike babu annashuwa, a ranar Laraba din ya fito yana ta murmushi yayin da suke daukan hoto da Atikun bayan ganawar sirri da suka yi, a halin yanzu ba a san abin da suka tattauna ba.

Kara karanta wannan

2023: Atiku ya nemi hadin kan Wike, Saraki da sauran jiga-jigan PDP don lallasa APC

Atiku ya wallafa hotuna a shafinsa na Twitter yana mai cewa ya karbi bakuncin Gwamna Nyesom Wike da wasu shugabannin PDP a gidansa kuma ya yi godiya bisa goyon bayan da suka bashi don ganin sun yi nasara a zaben da ke tafe domin ceto Najeriya.

2023: Da Yardar Allah Ni Da Kai Zamu Fafata a Zaɓen Shugaban Kasa, Tinubu Ya Taya Atiku Murna

A wani rahoton, jagoran jam'iyyar APC na ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya taya tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar nasarar lashe zaben fidda gwani na shugaban kasa karkashin inuwar jam'iyyar PDP na zaben 2023, Daily Trust ta rahoto.

Atiku ne ya samu ƙuri'u mafi rinjaye a zaben fidda gwanin da aka yi a Moshood Abiola Stadium Abuja ranar Asabar.

Tinubu ya jinjina wa Atiku bisa kishin kasarsa da jajircewa wurin ganin cigaban Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel