Gwamnonin jam'iyyar PDP 11 sun yi ganawar sirri a garin Asaba
- Gwamnonin jam'iyyar PDP 11 sun yi ganawar sirri a garin Asaba
- Ganawar hadda kwamitin gudanarwar jam'iyyar watau National Working Committee, NWC
- Ba'a samu cikakken bayani kan abun da suka tattauna ba amma dai bai wace zaben 2019
Labarin da muke samu daga majiyoyin mu sun tabbatar mana da cewa akalla gwamnonin jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party PDP a takaice ne suka yi wani taron ganawa na bayan labule da kwamitin gudanarwar jam'iyyar watau National Working Committee, NWC a takaice a garin Asaba na jihar Delta.
KU KARANTA: APC ta shiga hargitsi a kasar yarbawa game da 2019
Gwamnonin da suka halarci taron dai sun hada da Alhaji Hassan Damkwambo (Gombe), David Umahi (Ebonyi), Siareke Dickson (Bayelsa), Udom Emmanuel (Akwa-Ibom), Nyesom Wike (Rivers).
Sauran sun hada da Ayodele Fayose (Ekiti), Okezie Ikpazu (Abia), Darius Ishaku (Taraba), Ifeanyi Ugwuanyi (Enugu), Ben Ayade (Cross Rivers) sai kuma mai masaukin baki , Ifeanyi Okowa (Delta).
Har ya zuwa yanzu dai ba'a samu cikakken bayani kan abun da suka tattauna ba amma dai bai wace zaben 2019.
A wani labarin kuma, Shugaban jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya Yarima Uche Secondus a jiya Lahadi ya bayyana kungiyar nan da tsohon shugaban kasar farko na Najeriya a wannan jamhuriyar watau Cif Olusegun Obasanjo a matsayin wadda ba zata yi wa jam'iyyar su barazana ba a zaben 2019.
Secondus ya bayyana hakan ne a garin Asaba na jihar Delta yayin da reshen jam'iyyar na jihar ya tarbe shi jim kadan kafin fara taron su na kwamitin zartarwar jam'iyyar.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng