Kaduna: An Sako Ƴar Dr Ramatu Bayan Shafe Kwana 38 a Hannun Ƴan Bindiga

Kaduna: An Sako Ƴar Dr Ramatu Bayan Shafe Kwana 38 a Hannun Ƴan Bindiga

  • Masu garkuwa da mutane da suka sace malamar Kaduna Polytechnic, Dr Ramatu Abarshi da yarta da direbanta sun sako yar ta mai suna Ameera
  • Sun sako Ameera ne bayan ta shafe kwanaki 38 a hannunsu tana tsare kimanin kwana biyar bayan sako direban mahaifiyarta mai suna Ibrahim
  • Wata majiya da ta tabbatar da afkuwar lamarin ta ce tuni dai an sada Ameerah da iyalanta kuma an kai ta wani asibiti da aka boye sunansa domin a duba ta

Kaduna - Ameerah, yar malaman Kwalejin Fasaha ta Kaduna, Kad Poly, Dr Ramatu Abarshi, da aka sace ta shaƙi iskan yanci bayan kwana 38 a hannun yan bindiga.

An sako ta ne a ranar Talata an kuma kai ta wani asibiti da ba a bayyana sunansa ba domin duba lafiyarta, a cewar wata majiya, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Almundahanan Akanta Janar N80bn: Duk laifin Buhari ne, Buba Galadima

An Sako Dr Ramatu Bayan Shafe Kwana 38 a Hannun Yan Bindiga a Kaduna
An sako yar malaman Kad Poly bayan kwana 38 a hannun yan bindiga. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daily Trust ta rahoto cewa an sace Dr Abarshi da ƴarta da direbanta, Ibrahim a ranar 24 ga watan Afrilun 2022 a babban hanyan Kachia-Kaduna yayin da suke dawowa daga wurin rabon kayan sadaka.

Yayin da ita aka sako ta makonni uku da suka gabata, an sako direbanta a makon da ya wuce yayin da ita kuma yarta aka sako ta kwana biyar bayan sakin direban.

"Eh, an sako ƴar Ameerah a yammacin ranar Talata; an sada ta da yan uwanta kafin aka kai ta wani asibiti don duba lafiyarta. Abin ba sauki amma mun gode wa Allah cewa ta dawo gida lafiya," in ji shi.

Majiyar ta shaidawa Daily Trust cewa masu garkuwar sun karbi miliyoyi a matsayin fansa kafin sakinsu.

'Yan Ta'addan Da Suka Kai Hari Sansanin Sojoji Na Kaduna Sun Ɗanɗana Kuɗarsu, Lai Mohammed

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kashe makiyaya 4, sun sace shanaye 60 a Anambra

A bangare gudan, Gwamnatin Tarayya, a ranar Laraba ta ce yan ta'addan da suka kai hari sansanin sojoji da ke Birnin Gwari a Kaduna sun sha azaba a hannun sojoji a yayin da suka fatattake su, rahoton Daily Trust.

Ministan Labarai da Al'adu, Alhaji Lai Mohammed, ne ya bayyana hakan yayin da ya ke amsa tambayoyi kan tsaro bayan taron FEC da Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta a Aso Villa a Abuja.

Rahotanni sun bayyana cewa sojoji 11 ne suka riga mu gidan gaskiya yayin da wasu da dama suka jikkata yayin harin na ranar Talata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel