Yadda ta kaya da Tinubu ya bayyana gaban kwamitin tantance masu neman takara a APC

Yadda ta kaya da Tinubu ya bayyana gaban kwamitin tantance masu neman takara a APC

  • A jiya kwamitin tantance masu takarar shugaban kasa ya zauna da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
  • Ahmed Tinubu ya yi bayanin abin da ya sa yake neman takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC
  • Bayo Adenuga ya ce mai takarar ya nuna irin zurfin ilminsa wajen sanin tattalin arzikin Najeriya

Abuja - A ranar Litinin, 30 ga watan Mayu, 2022, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya zauna gaban kwamitin da ke tantance ‘dan takarar shugaban kasa a PDP.

The Cable ta fahimci Asiwaju Bola Ahmed Tinubu yana cikin wadanda kwamitin da John Oyegun yake jagoranta ya fara tantancewa cikin masu neman takara.

Mutane 11 aka tantance a jiya, Bola Tinubu da mutanensa sun isa otel din a lokacin ana ruwan sama.

Shugaban kwamitin yakin neman zaben Tinubu, Bayo Adenuga ya bayyana cewa mai gidansa ya yi wa kwamitin APC bayanin abin da ya sa yake neman mulki.

A cewar Bayo Adenuga, Bola Tinubu ya kawo nasarorin da ya samu a lokacin da ya mulki jihar Legas a cikin dalilan da suka sa yake so jam’iyyar ta tsaida shi.

A jawabin da Adenuga ya fitar, ya bayyana cewa Tinubu ya burge ‘yan kwamitin a game da yadda ya rika amsa tambayoyin da aka yi masa, yana bayani da kyau.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Tinubu na neman takara a APC
Wajen tantance Bola Tinubu Hoto: www.thecable.ng
Asali: UGC

Jawabin Bayo Adenuga

“Wasu tambayoyin sun shafi tasowarsa, ilminsa da aikin da ya yi. Ya fadawa kwamitin cewa ya cancanci ya zama ‘dan takarar shugaban kasa a APC.”
“Ya bada misali da nasarorinsa a matsayin gwamnan jihar Legas, inda ya kara harajin da ake samu daga N600m a duk wata, yanzu ya zama N51bn a yau.”
“Ya kuma kawo yadda ya gayyaci Enron da suka zama kamfanin farko da suka fara samar da wuta a Najeriya, da yadda Najeriya za ta samu lantarki.”

“A amsoshin da ya bada, Tinubu ya nuna zurfin ilminsa a bangaren tsimi da fahimtar tattalin arziki.”
“Kwamitin tantancewar sun gamsu da ilmin Tinubu game da tattalin arzikin Najeriya da sha’anin zamantakewar rayuwar da ke addabar Najeriya.”

- Bayo Adenuga

Bayan an kammala tantance tsohon gwamnan na jihar Legas, jaridar ta samu labari cewa ya dauki hoto tare da John Oyegun da sauran ‘yan kwamitin APC.

Takarar Atiku a PDP

Dazu kun ji cewa Gwamnoni jihohi biyu ake kawowa a lissafin wanda za su iya takarar mataimakin shugaban kasa PDP, su na shirin barin mulki.

Daga ciki akwai Gwamna Udom Emmanuel wanda ya nemi tikitin shugaban kasa a PDP, amma duk da haka Wazirin Adamawa na tunanin tafiya da shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel