Ayu ga Tambuwal: Kai ne gwarzon babban taron jam'iyyar PDP

Ayu ga Tambuwal: Kai ne gwarzon babban taron jam'iyyar PDP

  • Shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Iyorchia Ayu, ya yaba ma Gwamna Aminu Tambuwal kan rawar ganin da ya taka a zaben fidda dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar
  • Ayu ya bayyana Tambuwal wanda ya janyewa Atiku Abubakar a takarar fidda gwanin jam'iyyar a matsayin gwarzon taron
  • Atiku dai ya yi nasarar mallakar tikitin takarar shugaban kasa na PDP na babban zaben 2023 mai zuwa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Shugaban jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na kasa, Iyorchia Ayu, ya jinjinawa gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal, kan rawar ganin da ya taka a zaben fidda dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar da aka kammala, The Cable ta rahoto.

Jam’iyyar PDP ta gudanar da babban taronta na musamman a ranar Asabar don zabar dan takararta na shugaban kasa a zaben 2023 mai zuwa.

Kara karanta wannan

Shugabancin kasa a 2023: Wike da wasu 'yan siyasa 4 da ka iya zama abokan takarar Atiku

Yayin da yake jawabi a taron, Tambuwal, wanda shima yana cikin masu neman tikitin, ya sanar da janyewa daga tseren inda ya bukaci magoya bayansa da su marawa tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar baya.

A karshen zaben, Atiku ya samu kuri’u 371 kuma an ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben, yayin da Nyesom Wike, gwamnan jihar Ribas ya samu kuri’u 237.

Ayu ga Tambuwal: Kai ne gwarzon zaben fidda gwanin jam'iyyar PDP
Ayu ga Tambuwal: Kai ne gwarzon zaben fidda gwanin jam'iyyar PDP Hoto: The Cable
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tsohon shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki ne ya zo na uku da kuri’u 70, sai Udom Emmanuel, gwamnan jihar Akwa Ibom da kuri’u 38 yayin da Bala Mohammed na jihar Bauchi ya samu kuri’u 20.

Da yake magana a ranar Lahadi lokacin da ya ziyarci Tambuwal, shugaban PDP na kasa ya jinjina ma kokarinsa a yayin babban taron, rahoton Nigerian Tribune.

Yayin da yake rike da hannun Tambuwal, Ayu ya fada masa:

Kara karanta wannan

Shugaban kasa: Nasarar Atiku babban kalubale ne ga APC a 2023 – Orji Kalu

“Nagode. Kai ne gwarzon babban taron.”

Yan sanda sun kama yan yankan aljihu 10 a wajen zaben fidda dan takarar shugaban kasa na PDP

A wani labarin, mun ji cewa yan sanda sun damke wasu mutane 10 da ake zaton yan yankan aljihu ne a babban taron jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da aka yi a Abuja a ranar Asabar, 28 ga watan Mayu.

Wani jami’an dan sanda, Sufeto Maina Gambo ya fada ma kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) a kofar ‘gate D’ na filin wasa na Moshood Abiola, cewa an kama yawancin wadanda ake zargin ne a yayin da suke tsaka da yankawa mutane aljihu.

NAN ta kuma nakalto Gambo yana cewa an kwashi yawancin wadanda ake zargin zuwa ofishin yan sanda don bincike da hukunta su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel