Ainahin dalilin da yasa Tambuwal ya janyewa Atiku – Kungiyar yakin neman zabensa

Ainahin dalilin da yasa Tambuwal ya janyewa Atiku – Kungiyar yakin neman zabensa

  • Bayanai sun fito kan ainahin dalilin da yasa Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya janyewa tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar a zaben fidda gwanin PDP
  • Mai magana da yawun kungiyar kamfen din Tambuwal, Prince Daniel, ya ce gwamnan na jihar Sokoto ya janyewa Atiku ne saboda kishin kasa da son ci gaban Najeriya
  • Atiku dai ya yi nasarar mallakar tikitin takarar shugaban kasa na PDP bayan Tambuwal ya janye masa sannan ya samu kuri'u 371

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kakakin kungiyar yakin neman zaben Tambuwal, Prince Daniel, ya bayyana dalilan da suka sa gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal, ya janyewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, a yayin zaben fidda dan takarar shugaban kasa na PDP.

Legit.ng ta rahoto cewa bayan janye masa da Tambuwal ya yi, Atiku ya lashe zaben da kuri’u 371 inda ya kayar da babban abokin takararsa Gwamna Nyesom Wike na jihar Rivers wanda ya samu kuri’u 237.

Kara karanta wannan

Ba zan yi amai na lashe ba: Martanin gwamna Wike da ya sha kaye bayan ganawa da Atiku

Daniel, a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, ya ce Tambuwal ya janye ne saboda kishin kasa da son ganin ci gaban Najeriya, jaridar The Punch ta rahoto.

Ainahin dalilin da yasa Tambuwal ya janyewa Atiku – Kungiyar yakin neman zabensa
Ainahin dalilin da yasa Tambuwal ya janyewa Atiku – Kungiyar yakin neman zabensa Hoto: Atiku Abubakar, Aminu Waziri Tambuwal
Asali: Facebook

Sanarwar ta ce:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“Hukuncin Tambuwal na janyewa daga tseren duk da cewar shi ke da damar mallakar tikitin ya kasance ne saboda tsananin sonsa ga Najeriya musamman ma ga jam’iyyar.
“Zuwa ga tarin magoya bayanmu, muna so ku sani cewa mun dauki wannan hukuncin ne saboda kishin kasa, inda muka sanya kasarmu Najeriya da jam’iyyarmu sama da ra'ayin kanmu wanda muka nanata cewa bai kai ra’ayin kasarmu ba.
“Mai girma gwamna na matukar godiya ga shugaban kungiyar kamfen dinsa kan kyakkyawan jagorancinsa, da daukacin tawaga da dukkanin deleget da dimbin magoya bayansa a fadin kasar nan kan goyon bayansu gare shi kafin babban taron, da yayin taron da kuma bayan taron.

Kara karanta wannan

Ayu ga Tambuwal: Kai ne gwarzon babban taron jam'iyyar PDP

“Ya roki Allah ya yiwa PDP jagora da bata nasara yayin da jam’iyyar ke aiki don ceto Najeriya daga mulkin kama karya na tsawon shekaru da gwamnatin APC ta yi.”

Ayu ga Tambuwal: Kai ne gwarzon babban taron jam'iyyar PDP

A gefe guda, shugaban jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na kasa, Iyorchia Ayu, ya jinjinawa gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal, kan rawar ganin da ya taka a zaben fidda dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar da aka kammala, The Cable ta rahoto.

Jam’iyyar PDP ta gudanar da babban taronta na musamman a ranar Asabar don zabar dan takararta na shugaban kasa a zaben 2023 mai zuwa.

Yayin da yake jawabi a taron, Tambuwal, wanda shima yana cikin masu neman tikitin, ya sanar da janyewa daga tseren inda ya bukaci magoya bayansa da su marawa tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar baya.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa: Nasarar Atiku babban kalubale ne ga APC a 2023 – Orji Kalu

Asali: Legit.ng

Online view pixel