Da duminsa: Dan takarar gwamnan APC ya fice daga jam’iyyar, ya ce sai ya yi takara a 2023

Da duminsa: Dan takarar gwamnan APC ya fice daga jam’iyyar, ya ce sai ya yi takara a 2023

  • Sakamakon zaben fidda gwanin dan takarar gwamnan APC da aka kammala a jihar Oyo ya sanya Adebayo Adelabu da magoya bayansa ficewa daga jam’iyyar
  • Adelabu wanda ya rasa tikitin APC don shiga tseren babban zaben na 2023 ya sanar da ficewarsa daga APC a ranar Lahadi, 29 ga watan Mayu
  • Sai dai, dan siyasar ya ce sai ya yi takara a babban zaben na 2023, inda yace nan ba da dadewa ba zai koma wata jam’iyyar

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Oyo - Cif Adebayo Adelabu, wanda aka fi sani da Penkelemes, ya fice daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC) tare da wasu fusatattun shugabannin jam’iyyar.

Adelabu ya kasance dan takarar gwamna na APC a 2019 amma ya sha kaye a hannun Sanata Teslim, Folarin a zaben fidda gwanin jam’iyyar na 2023 da aka kammala kwanan nan.

Kara karanta wannan

Gwamnan Plateau: Masu neman tikitin APC 18 sun yi watsi da zaben fidda gwanin jam’iyyar

Wasu shugabannin APC a Oyo da Adelabu sun sanar da sauya shekarsu a ofishin kamfen din Adelabu da ke Ibadan, babbar birnin jihar a ranar Lahadi, 29 ga watan Mayu.

Da duminsa: Dan takarar gwamnan APC ya fice daga jam’iyyar, ya sha alwashin yin takara a zabe mai zuwa
Da duminsa: Dan takarar gwamnan APC ya fice daga jam’iyyar, ya sha alwashin yin takara a zabe mai zuwa Hoto: Bayo Adelabu
Asali: Facebook

Yayin da yake jawabi, Adelabu ya sha alwashin yin takara a zaben gwamna na 2023 sannan ya baiwa magoya bayansa tabbacin samun nasara a zaben.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce:

“Za mu kasance masu nasara. Za mu ceto jihar Oyo a shekara mai zuwa. Za mu yi nasara a 2023.”

Folarin, mai wakiltan Oyo ta tsakiya a majalisar dattawa, ya lallasa Adelabu da kuri’u 954.

Adelabu ya samu kuri’u 327 inda ya zo na biyu a zaben.

Babu Jonathan: Jerin sunayen yan takarar shugaban kasa 23 da APC za ta tantance

A wani labari na daban, mun ji cewa babu sunan tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan a jerin masu neman takarar shugaban kasa da ake sanya ran jam’iyyar All Progressives Congress (APC) za ta tantance.

Kara karanta wannan

2023: Dattijo ya lashe tikitin APC na sanata mai wakiltan Kaduna ta tsakiya

A watan Afrilu ne magoya bayansa suka yiwa gidansa na Abuja tsinke inda suka nemi ya tsaya takarar shugaban kasa na 2023, amma Jonathan bai yi martani ba.

Yan kwanaki bayan nan, wata kungiya ta Arewa ta siya masa fom din takara ta APC amma tsohon shugaban kasar ya karyata amincewa da siya masa fom din.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng