Gwamnan Plateau: Masu neman tikitin APC 18 sun yi watsi da zaben fidda gwanin jam’iyyar

Gwamnan Plateau: Masu neman tikitin APC 18 sun yi watsi da zaben fidda gwanin jam’iyyar

  • Yan takarar kujerar gwamna karkashin inuwar APC a jihar Plateau sun yi watsi da sakamakon zaben fidda gwanin jam'iyyar
  • An dai bayyana Nentawe Yilwatda a matsayin wanda ya yi nasara a zaben fidda gwanin domin daga tutar APC a zaben 2023 mai zuwa
  • Fusatattun yan takarar sun yi zargin cewa ba a bi ka'idojin da ya dace ba a zaben, don haka sun nemi a sake sabon zabe

Plateau - Masu neman tikitin takarar gwamnan jihar Plateau a zaben fidda gwanin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da aka kammala kwanan nan sun yi zanga-zanga a kan bayyanar Nentawe Yilwatda a matsayin wanda ya lashe zaben.

Masu takarar sun nuna rashin jin dadinsu da kin amincewa da zaben fidda gwanin a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun sakataren kungiyar manema tikitin na APC a Filato, Danyaro Sarpiya.

Kara karanta wannan

Zaben fidda gwanin PDP: Har yanzu akwai damar fitar da dan takarar maslaha – Shugaban kwamitin amintattu

Jawabin da aka gabatarwa da kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) a Jos ya yi zargin cewa gaba daya tsarin bai yi daidai da ka’idojin jam’iyyar APC na fitar da ‘yan takara a zaben 2023 ba.

Gwamnan Plateau: Masu neman tikitin APC 18 sun yi watsi da zaben fidda gwanin jam’iyyar
Gwamnan Plateau: Masu neman tikitin APC 18 sun yi watsi da zaben fidda gwanin jam’iyyar Hoto: Vanguard
Asali: UGC

Sun yi watsi da ikirarin cewa an gudanar da zaben fidda dan takarar gwamnan a ranar 26 ga watan Mayu, cewa an soke zaben kuma ya kamata a ajiye shi a gefe, rahoton Premium Times.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sun yi kira ga sake nazarin tarukan jam’iyyar daga matakin unguwa don samun damar zaben deleget a tsanake don shiga sabon zaben fidda gwani da zai haifar da sahihin dan takara.

“Mun rubuta takardar daukaka kara ga kwamiyin daukaka kara domin magance wannan zambar don kare APC a Plateau.
“Hujjarmu ta daukaka karar ya karkata ga cewar ba a yi zaben deleget ba kuma ana ta yiwa jerin sunayen deleget din kwaskwarima da canjin karshe da aka yi a ranar zaben fidda gwani.

Kara karanta wannan

Kano: An Yi Yunƙurin Kashe Ni Yayin Zaɓen Fidda Gwani, Ban Yarda Da Zaɓen Ba, Ɗan Takarar Gwamnan APC

“An kange wadannan deleget da ake magana a kansu daga masu rike da mukaman siyasa da shugabannin kananan hukumomi.
“A yayin zaben fidda gwanin, wasu mutane marasa izini sun kasance a wajen zaben don tsoratar da mutane da bibiyar kuri’un deleget.”

Yan takarar sun tuna cewa sun tabo muhimman batutuwa a taron manema labarai da aka yi a ranar 9 ga watan Mayu, kuma sun sanar da duniya shirin tursasa Yilwatda a kan jam’iyyar.

Kokarin jin martanin APC reshen Plateau ya ci tura domin sakataren labarai ta, Sylvanus Namang, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) cewa harkoki sun sha kansa saboda zaben fidda gwanin sanatan APC.

2023: Bayan siyan fom din APC na N50m, dan takarar gwamna daga wata jihar Arewa ya sauya sheka

A wani labari, mun ji a baya cewa wani dan takarar gwamna a jihar Plateau, Ambasada Yohana Margif, ya fice daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki.

Kara karanta wannan

Sokoto: Ƴan Takarar APC Sun Fice Daga Wurin Zaɓen Fidda Gwani a Fusace Bayan Ɗaukewar Wutar Lantarki

Margif, wanda ya siya fom din takara na zaben gwamna, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar a cikin wata sanarwa da ya saki ga manema labarai a garin Jos, a ranar Laraba, 18 ga watan Mayu, jaridar Punch ta rahoto.

Har ila yau, ya sanar da hukuncin da ya yanke a cikin wata wasika wanda aka gabatawar shugaban APC na gundumar Margif/Kopmur da ke Mushere, karamar hukumar Bokkos, wadda aka mika kwafinta ga shugabannin APC na karamar hukuma da na jaha.

Asali: Legit.ng

Online view pixel