Daga karshe: APC ta sanar da ranar tantance 'yan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar
- Jam'iyyar APC mai mulki ta sanar da cewa za ta tantance wadanda suka siya fom din takarar shugabancin kasa a ranakun Litinin da Talata
- Wannan na zuwa ne bayan da jam'iyyar ta sanar da cewa za ta yi zaben fidda dan takarar shugabancin kasanta a ranakun 6 da 8 ga Yuni masu zuwa
- A halin yanzu, jam'iyyar za ta tantance 'yan takara 23, 11 daga ciki ranar Litinin yayin da sauran 12 sai ranar Talata mai zuwa
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Abuja - Jam'iyyar APC ta sanya ranar Litinin da Talata su zama ranakun tantance wadanda suka siya fom din takarar shugabancin kasa a karkashin inuwar jam'iyyar.
Kamar yadda jerin sunayen da jam'iyyar ta bayyana a ranar Lahadi, jimillar 'yan takara 23 ne suka siya fom kuma ake tsammanin ganinsu a wurin tantancewar, The Cable ta rahoto.
Za a tantance 'yan takara 11 a ranar Litinin yayin da sauran 12 za a tantance su a ranar Talata mai zuwa.
Wannan cigaban na zuwa ne bayan an dage tantancewar da aka sanya za a yi ta tun a makon da ya gabata.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Har zuwa safiyar Juma'a, sa'o'i kadan kafin a sauya ranar zaben fidda gwani na 'yan takarar shugabancin kasar, ba a saka ranar tantancewar ba.
An sanya za a yi zaben fidda gwani na jam'iyyar APC a ranakun 29 da 30 na watan Mayun da farko.
Sai dai, a ranar Juma'a da ta gabata, Hukumar Zabe mai zaman kanta ta INEC ta sanar da kara wa'adin da ta bai wa jam'iyyun siyasa da su yi zabukan fidda gwanayensu zuwa ranar 3 ga watan Yuni bayan taron da ta yi da Majalisar Shawari ta Jam'iyyu, IPAC.
A halin yanzu, INEC ta bai wa jam'iyyun siyasa har zuwa ranar 9 ga watan Yuni da su kammala dukkan abubuwan da suka shafi zabukan fidda gwani na zaben 2023 mai zuwa.
Bayan dage wa'adin zabukan fidda gwanin da hukumar ta yi, APC ta sanar da dage ranakun zabukan fidda gwaninta.
A halin yanzu, za a yi zaben fidda gwani na 'yan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar APC a ranakun 6 da 8 na watan Yuni a Abuja.
An gano dalilin da yasa APC ta gaza tantance masu takarar shugabancin kasa a jam'iyyar
A wani labari na daban, akasin rahotannin da ke yawo kan tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan na cewa ya fita daga jerin masu takarar shugabancin kasa a jam'iyyar APC saboda bai mayar da fom din takararsa ba, Vanguard ta tattaro cewa yana nan daram cikin 'yan takara.
Majiyoyi sun ce ya mayar da fom din har ofishin jam'iyyar. Sai dai shugabannin jam'iyyar sun gaza tabbatar da cewa ko ya bar jam'iyyar PDP ko kuma yana nan har yanzu.
Asali: Legit.ng