An gano dalilin da yasa APC ta gaza tantance masu takarar shugabancin kasa a jam'iyyar

An gano dalilin da yasa APC ta gaza tantance masu takarar shugabancin kasa a jam'iyyar

  • Majiyoyi masu karfi sun tabbatar da cewa Goodluck Jonathan yana daga cikin dalilin da suka sa har yau ba a tantance 'yan takarar shugabancin kasa na APC ba
  • Duk da Buhari bai bayyana matsayarsa kan takarar Jonathan a APC ba, akwai yuwuwar ya samu takarar shugabancin kasa kuma ya yi nasarar komawa Villa
  • Majiya makusanciya da Jonathan ta sanar da yadda wasu 'yan siyasan arewa suke shige da fice tare da fafutukar ganin Jonathan ya koma Aso Villa

Akasin rahotannin da ke yawo kan tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan na cewa ya fita daga jerin masu takarar shugabancin kasa a jam'iyyar APC saboda bai mayar da fom din takararsa ba, Vanguard ta tattaro cewa yana nan daram cikin 'yan takara.

Majiyoyi sun ce ya mayar da fom din har ofishin jam'iyyar. Sai dai shugabannin jam'iyyar sun gaza tabbatar da cewa ko ya bar jam'iyyar PDP ko kuma yana nan har yanzu.

Kara karanta wannan

2023: Atiku Ya Bayyana Manufofi 5 Da Zai Yi Amfani Da Su Don Tsallakar Da Najeriya Zuwa Ga Tudun Mun Tsira

Wasu daga cikin shugabannin PDP da suka samu jagorancin Gwamna Samuel Ortom na jihar Benuwe a farkon makon nan sun gana da Jonathan domin shawo kansa kan ya zauna a PDP kuma ya halarci taronsu da za a yi a ranar Asabar.

An gano dalilin da yasa APC ta gaza tantance masu takarar shugabancin kasa a jam'iyyar
An gano dalilin da yasa APC ta gaza tantance masu takarar shugabancin kasa a jam'iyyar. Hoto daga vanguardngr.com
Asali: UGC

Kokarin saka Jonathan cikin 'yan takarar kamar yadda majiyoyi suka tabbatar a daren jiya yana daga cikin dalilan da suka sa aka dage tantance 'yan takarar shugabancin kasa na APC.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Baya ga kokarin kafa kwamitin mutum bakwai na tantancewar wanda shugaban jam'iyyar na kasa, Sanata Abdullahi Adamu zai shugabanta, dole ne basu jerin sunayen 'yan takarar da za a tantance.

An tattaro cewa, a kokarin wasu jiga-jigan jam'iyyar na arewa wurin janyo hankalin Jonathan zuwa shugabancin kasa a 2023, hakan yana daga cikin abinda yasa ake jan kafa kan tantance 'yan takarar.

Kara karanta wannan

Shehu Sani: Dan takarar PDP ya kwato N100m daga hannun deleget ta hanyar amfani da mafarauta da ’yan banga

A daren jiya Vanguard ta gano cewa, duk da an tura shawarar gaban shugaban kasa Muhammadu Buhari, bai taba watsi da ita ba ko kuma ya bayyana cewa yana goyon bayan hakan ba.

Wata majiya kusa da tsagin Jonathan ta tabbatar wa da Vanguard cewa tabbas kokarin da ake yi shi ne a ga Jonathan ya samu takarar shugabancin kasa a 2023 karkashin APC, amma sai dai ya ki cigaba da bayar da bayani.

Majiyar ta tabbatar da cewa, idan aka cire duk wani rashin tabbaci na siyasa, akwai yuwuwar tsohon shugaban kasan ya zama dan takarar APC kuma ya ci zaben shugabancin kasa a zaben 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel