Gumi ga Deliget: Cin hancin da za ku karba ba zai kare ku daga rashin tsaron Najeriya ba
- Fitaccen malamin addinin Islama, Sheikh Ahmad Gumi ya yi kira ga deliget kan su yi zaben shugabanni nagari ba domin sullala ba
- Ya kara da ankarar da su cewa, cin hancin da za su karba ba zai tseratar da Najeriya daga rashin tsaron da ta ke ciki ba
- Ya bukaci wakilan jam'iyyun da su fifita ra'ayin kasa sama da nasu ra'ayin ko na 'yan siyasa masu son kansu
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Kaduna - Fitaccen malamin addinin Islama, Ahmad Gumi, ya ja kunnen deliget din jam'iyyu da su guji karbar cin hanci wurin zaben 'yan takarar jam'iyyunsu.
Gumi a wata takardar da ya fitar, ya ja kunne kan cewa "duk wani dan kabila ko mai rajin a ware ko da kuwa zai bayar da hanci don ya samu mulki, zai tarar da Najeriya ta yadda ba zai iya juya ta ba kuma ta gagaresa kuma daga karshe dukkanmu ne za mu wahala."
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce, dan kudin da ake bai wa deliget na cin hanci ba za su iya karemu daga tashin tsaro ko rashin daidaituwar Najeriya ba da zai cigaba idan aka sani wadanda ba su dace ba, Premium Times ta rahoto.
Ya shawarci deliget da su kasance masu tunani yayin zaben shugabannin kuma kada 'yan sulalla su rufe musu ido su yi zaben wanda bai dace.
Ya ce ra'ayin kasa ya dace ya sha gaban son kai da zarinsu. Su zabi wadanda suka dace kuma suke da gogewa a shugabanci, ba 'yan koyo ba ko 'yan siyasa masu ganganci wadanda ke da burin nawa jiragen shugaban kasa.
Zaben 2023: Jam'iyyar PDP ta fi APC tsoron Allah - Gwamna Fintiri
A wani labari na daban, Gwamna Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa ya yi imani da cewa PDP ita ce mafita ga 'yan Najeriya a kan jam'iyya mai mulki (APC) kuma PDP ta fi APC tsoron Allah.
Gwamnan ya zanta da Channels Television a game da gangamin zaben PDP na kasa, wanda ake gabatarwa a ranar Asabar a Abuja. Yayin da ya amince da cewa jam'iyyar ta yi kuskure a baya, amma duk da haka ita PDP ta zarcewa APC.
"Sun riga sun yafe mana sannan ina tunanin ta mu (PDP) ta fi ta su. Mun fi APC tsoron Allah," gwamnan ya bayyana hakan ne a wani taro da aka gabatar a Mashood Abiola Stadium Velodrome a Abuja."
Asali: Legit.ng