Ina da lafiya, ai ba dan dambe ake bukata a Aso Rock ba: Tinubu

Ina da lafiya, ai ba dan dambe ake bukata a Aso Rock ba: Tinubu

  • Asiwaju Bola Ahmed Tinubu karo na biyu ya yi magana kan kalaman da ake na cewa bai da isasshen lafiya
  • Tinubu wanda ke yawon yakin neman zaben delegets yace kwakwalwar mutum ake bukata ba karfinsa ba
  • Ya ce masu cewa ba shi da lafiyan jiki, su ke da matsalar kwakwalwa saboda basu da hankali

Akure - Jagoran jam'iyyar All Progressives Congress kuma dan takaran kujeran shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa yana cikin koshin lafiya kuma shirya yake ya mulki Najeriya a 2023.

Ya ce abinda Najeriya ke bukata shine shugaba mai kwakwalwa da kwazo wanda zai iya fuskantar kalubalen da kasar ke fama musamman tattalin arziki.

Punch ta ruwaito Tinubu na fadin hakan ne yayinda yake jawabi ga deleget na jihar Ondo a ziyarar yakin neman zabe da ya kai Akure ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

An damke yaran siyasan Aisha Binani suna rabawa Deleget makudan kudi a Adamawa, Hotuna

Ya ce ba dan dambe ake bukata ba, saboda haka yana da lafiyar mulkar Najeriya.

Yace:

"Ban shiga neman kujerar shugaban kasa don bukatar kudi ba, ina takara ne don soyayyar da nikewa kasar nan, don siyasar jama'a ta da kuma muhimmancin da na baiwa ilimi da cigaba."

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Ba aikin dambe nike nema ba, ba Anthony Joshua zan tafi fuskanta a fadar shugaban kasa ba, ba takara da Ronaldo nike ba. Da kwakwalwata kawai zan yi amfani."

Tinubu
Ina da lafiya, ai ba dan dambe ake bukata a Aso Rock ba: Tinubu Hoto: Asiwaju
Asali: Twitter

Masu cewa ba ni da isasshen lafiya basu da hankali, mahaukata ne: Tinubu

A kwanakin baya, Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa mutum mai hikima da kwazo ake bukata matsayin shugaba ba lebura ko maji karfi ba.

A kalamansa, aikin shugaban kasa ba na hawa kan tsauni bane ko diban kankare, aikinsa tunani da amfani da kwakwalwarsa.

Kara karanta wannan

2023: Wani Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a NNPP Ya Sallama Wa Kwankwaso, Amma Ya Nemi Wata Alfarma Daga Wurin Kwankwason

Tinubu ya bayyana hakan ne ranar Juma'a a Minna, yayinda ya tafi yawan kamfe wajen deleget na APC a jihar, rahoton Punch.

Tsohon gwamnan na Legas ya bayyanawa deleget din cewa masu zaginsa bisa rashin lafiyan da yayi basu da hankali irin nasa.

Tinubu ya kara da cewa ya sauya fasalin jihar Legas kuma ya gyarata, haka yake son yiwa Najeriya.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel