Hasashen tazarcen Zulum da wasu Gwamnonin PDP da APC 10 masu neman zarcewa a 2023

Hasashen tazarcen Zulum da wasu Gwamnonin PDP da APC 10 masu neman zarcewa a 2023

Akwai gwamnonin jihohi 11 da za su so su zarce a kan kujerun da suke kai a zabe mai zuwa.

Legit.ng Hausa ta yi nazarin halin da wadannan gwamnoni su ke ciki game da yiwuwar tazarcensu da barazanar da suke fuskanta daga sauran jam’iyyu.

Wadannan gwamnonin jihohi su ne:

1. Ahmadu Fintiri (Adamawa)

2. Bala Mohammed (Bauchi)

3. Babagana Zulum (Borno)

4. Muhammad Inuwa Yahaya (Gombe)

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

5. AbdulRahman AbdulRasaq (Kwara)

6. Babajide Sanwo-Olu (Lagos)

7. Abdullahi Sule (Nasarawa)

8. Dapo Abiodun (Ogun)

9. Seyi Makinde (Oyo)

10. Mai Mala Buni (Yobe) da

11. Bello Matawalle (Zamfara)

1. Adamawa

Tuni Gwamna Ahmadu Fintiri ya samu tikitin PDP, zai fuskanci babban kalubalensa ne daga wanda jam’iyyar APC ta tsaida a matsayin ‘dan takararta.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Mohammed Abacha ya lashe zaben fidda gwanin PDP na gwamna a Kano

A masu harin kujerar gwamna a jihar akwai tsohon gwamna Muhammad Jibrila Bindow, tsohon shugaban EFCC, Nuhu Ribadu da Hon. Abdulrazaq Namdas.

Abin da zai iya yiwuwa: APC za ta zo daf da karbe mulki.

2. Bauchi

Gwamnan Bauchi Bala Mohammed ya na neman takarar shugaban kasa a PDP. Idan bai yi nasara ba, babu mamaki zai dawo ya canji ‘dan takarar da aka tsaida a PDP.

Shi ma Sanata Bala Mohammed zai gwabza da wanda ya samu tikiti a APC da sauran jam’iyyu. Kamar yadda aka san siyasar Bauchi, komai zai iya faruwa a 2023.

Abin da zai iya yiwuwa: PDP za ta sha da kyar.

3. Borno

Farfesa Babagana Zulum yana neman zarcewa a ofis. A tarihi, PDP ba ta taba mulki a Borno ba, haka zalika Zulum yana da farin jinin da zai yi wahala a doke shi.

Abin da zai iya yiwuwa: PDP ba za ta tsira da komai ba.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Akanta janar din jihar Ribas ya lashe tikitin gwamnan PDP

4. Gombe

A jihar Gombe akwai kura a gaban Muhammad Inuwa Yahaya. Gwamnan ya samu sabani da babban ‘dan siyasan jihar, Sanata Muhammad Danjuma Goje a APC.

Wadanda za su yi takarar gwamnan Gombe a jam’iyyun hamayya sun hada da Muhammad Jibril Barde da Hamisu Mai lantarki a PDP da kuma NNPP da ta shigo gari.

Abin da zai iya yiwuwa: APC za ta zarce a kan mulki.

5. Kwara

Kamar dai a Gombe, shi ma AbdulRahman AbdulRasaq ya yi fada da kusoshin PDP a Kwara. A APC, zai fara da yakinsa da Gbemisola Saraki da Lai Mohammed.

Rikicin APC ya sa wasu ‘yan takara sun koma SDP a jihar. A PDP kuma su Bukola Saraki za su fito da ‘dan takarar gwamna daga Arewacin Kwara a wannan karo.

Abin da zai iya yiwuwa: PDP za ta kawo barazana a wasu yankuna, APC za ta tsira.

Gwamnan Borno, Zulum
Hoto: Gwamnan Borno, Farfesa Babagana Zulum Hoto: @profzulum
Asali: Twitter

6. Legas

Wata jiha da PDP ba ta taba mulki ba ita ce Legas, da alama Babajide Sanwo-Olu zai samu tikitin APC cikin ruwan sanyi ba kamar yadda aka yi a zaben 2019 ba.

Kara karanta wannan

Babu baraka a APC: Murtala Sule Garo ya karyata rade-radin sauya-sheka zuwa NNPP ko PDP

Gwamna Sanwo-Olu zai yi yaki da ‘yan adawan Tinubu da ke neman ganin bayansa da kuma Olajide Adediran wanda zai tsayawa PDP da ke cikin rigingimu.

Abin da zai iya yiwuwa: Za a maimaita abin da aka yi a baya.

7. Nasarawa

Abdullahi Sule ya yi alkawarin ba zai zarce a mulki ba, amma da alama zai saba rantsuwar da yayi. Babban kalubalensa shi ne gayyar da aka yi masa a PDP.

Abdullahi Adamu ba zai so ya rasa jiharsa ba, amma Labaran Maku, Nuhu Angbazo, Salomon Ewuga duk za su taru domin ganin David Ombugadu ya yi galaba.

Abin da zai iya yiwuwa: PDP ba za ta samu nasara ba.

8. Ogun

Ana zargin Gwamna Dapo Abiodun da cewa ya taba aikata laifi a kasar waje. A kan wannan wasu ‘yan APC suka huro wuta cewa a hana shi takara a jam’iyya mai mulki.

Ko Abiodun ya samu tikiti a APC, ba dole bane babban zabe ya zo masa da sauki domin za a ga tasirin Atiku Abubakar a Ogun tun da tsohon hadiminsa zai yi takara.

Kara karanta wannan

Abokin takararsu Atiku a zaben 2019, Dankwambo zai sake jarraba sa'ar zama Sanata

Abin da zai iya yiwuwa: APC za ta zarce.

9. Oyo

Injiniya Seyi Makinde ya samu tikitin jam’iyyar PDP a cikin sauki. Za a gwabza ne tsakaninsa da wanda jam’iyyar APC ta tsaida ya yi mata takara a zaben 2023.

Zuwa yanzu Sanata daya da PDP ta ke da shi a jihar Oyo ya koma jam’iyyar APC, amma babu mamaki matasa da tsofaffin ma’aikata su ceci tazarcen Makinde.

Abin da zai iya yiwuwa: PDP za ta cigaba da mulki.

10. Yobe

Bayan shekaru biyu, Mai Mala Buni ya ajiye shugabancin jam’iyyar APC, ya koma gida. Ana tunani a 2023, tarihi ne zai sake maimaita kansa yadda aka saba.

Abin da zai iya yiwuwa: PDP ba za ta tsira da komai ba.

11. Zamfara

Gwamna Bello Matawalle ya na kan hanyar zarcewa a kan mulki bayan dinke barakar APC a jihar Zamfara. Matawalle ba zai fuskanci kalubale a zaben gwani ba.

A halin yanzu Mahadi Gusau ya fasa yin takarar gwamna, hakan na nufin ba zai gwabza da mai gidansa a 2023 ba. Ko wanene ya samu tikitin PDP, yana da aiki!

Kara karanta wannan

Kujera na rawa: Sanatoci 12 da watakila ba za su koma Majalisar Dattawa bayan 2023 ba

Abin da zai iya yiwuwa: APC za ta zarce.

Isah Ashiru Kudan ya yi nasara a Kaduna

Dazu an samu rahoto babu canji a PDP ta jihar Kaduna, Isah Ashiru Kudan wanda ya rike tutar jam’iyya a 2019 shi ne zai sake tsayawa takara a zabe mai zuwa.

Har Sanata Shehu Sani ya taya wanda ya lashe zaben tsayawa takarar Gwamna a jam’iyyar PDP murnar samun nasara bayan an ji sakamakon zaben da asuba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel