Babu banbancin tsakanin Deleget da dan bindiga mai karbar kudin fansa, Shehu Sani

Babu banbancin tsakanin Deleget da dan bindiga mai karbar kudin fansa, Shehu Sani

  • Kwamred Shehu Sani ya bayyana cewa ya gwammace da ya fadi a zabe, da ya biya wani kudi don ya zabesa
  • Dan siyasan jihar Kadunan ya bayyana cewa da Deleget, da yan bindiga masu garkuwa da mutane duk daya suke
  • Shehu Sani yace bai jahilci yadda harkar deleget take amma da gayya yayi takara don tona musu asiri

Kaduna - Tsohon Sanata kuma mai neman zama Gwamna a Kaduna, Kwamred Shehu Sani, ya bayyana cewa babu banbanci tsakanin Deleget da yan bindiga masu garkuwa da mutane.

Shehu Sani ya bayyana hakan ne yayinda yake Alla-wadai da zaben fidda gwanin jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a Kaduna, rahoton Premium Times.

Sani, ya fadi warwas a zaben inda ya samu kuri'u biyu kacal.

Kara karanta wannan

2023: Dattijo ya lashe tikitin APC na sanata mai wakiltan Kaduna ta tsakiya

Ya bayyana cewa cin hanci da rashawa kawai akeyi a harkar zabe sannan a zabi mutanen da basu cancanta ba.

Ya lashi takobin cewa ba zai biya wani deleget ko sisi don a zabesa ba.

Shehu Sani
Babu banbancin tsakanin Deleget da dan bindiga mai karbar kudin fansa, Shehu Sani Hoto: Senator Shehu Sani
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yace:

"Ban yarda siyasar sai ka biya mutum ya zabeka ba. Wannan ya sabawa ka'idoji na da imani."
"Ina sane da irin lalacin dake cikin siyasarmu da yadda muka rungumi wannan lalaci."
"Na yi musharaka ne don tona asirin yadda abubuwa ke gudana da kuma bude filin tattauna yadda zamu ceto siyasarmu daga wajen barayi."
"Babu banbanci tsakanin yan bindiga masu karban kudin fansa da deleget masu karban kudi don zabe. Tufka da warwara ne mu rika kuka yan bindiga na karbar kudin fansa amma wasu deleget na karba kudi don zabe."

Shehu Sani ya sha kashi a zaben ‘dan takarar Gwamnan Kaduna, ya tsira da kuri’u 2

Kara karanta wannan

Fito na fito da Gwamna Bagudu: Adamu Aliero ya janye daga neman kujerar Sanata

Burin Shehu Sani na zama sabon gwamnan jihar Kaduna a 2023 ba zai cika ba, a sakamakon rashin nasarar da ya yi a zaben fitar da gwani.

Rahoton da muka samu ya tabbatar da cewa Sanata Shehu Sani bai iya samun tikitin PDP ba.

‘Dan siyasar ya tabbatar da wannan a Twitter da asuban ranar Alhamis. Sani ya taya wanda ya yi nasara murna, ya yabawa wadanda suka ba shi kuri'arsu.

Tsohon Sanatan ya sha kashi a hannun Honarabul Isah Ashiru Kudan a zaben fitar da ‘dan takarar da aka yi a ranar Laraba, 25 ga watan Mayu, 2022.

Asali: Legit.ng

Online view pixel